Zaben 2019: Ina kira ga jama'ata sun fito su zabi Buhari - Dan takaran gwamna, Salihu Takai

Zaben 2019: Ina kira ga jama'ata sun fito su zabi Buhari - Dan takaran gwamna, Salihu Takai

Dan takaran gwamnan jihar Kano karkashin jam'iyyar Peoples Redemption Party (PRP), Malam Salihu Takai, ya yi kira ga jama'an Najeriya su fito kwansu da kwarkwatansu domin kada kuri'arsu ranan Asabar, 2 ga watan Febrairu, 2019.

Malam Takai, wanda yayi wannan bayani ta bakin mai magana da yawunsa, Auwalu Mu'azu, ya ce ya yi wanna kira ne saboda yadda mutane suka fusata sakamakon dage zabe da hukumar gudanar da zabe wato INEC tayi.

Yace: "Bisa ga yadda ran yan Najeriya ya baci kan dage zaben da akayi, ya zama wajibi dukkanmu muyi aiki tukuru domin ganin cewa jama'a sun fitokwansu da kwarkwatarsu domin musharaka a zabe."

Bugu da kari, Malam Takai ya marawa shugaba Muhammadu Buhari goyon bayansa a zaben shugaban kasa domin ya cigaba da ayyukan kwarai da ya fara.

A bangare guda, Hukumar yan sandan jihar Kano ta damke wasu mutane 950 da ake zargi da bangan siyasa cikin kwanaki 9 da suka gabata.

Kwamishanan yan sandan jihar Kano, Wakili Mohammed, ya bayyana hakan ne ranan Talata da kwamitin zaman lafiya Kano suka kai masa ziyara. Ya ce an damke yan bangan siyasan ne a wurare daban-daban a fadin jihar.

Daga cikin yan daba 950 da aka kama, 750 na kurkuku a yanzu yayinda ake sauraron gurfanarsu a kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel