Kwankwaso yana so a harbe masu karya allon takarar PDP a Kano

Kwankwaso yana so a harbe masu karya allon takarar PDP a Kano

- Kwankwaso ya ja kunnen ‘Yan bangar siyasar da ke yi wa PDP barna a Kano

- Tsohon Gwamnan yace za su iya maganin tun daga Gwamnan zuwa kan kowa

Kwankwaso yana so a harbe masu karya allon takarar PDP a Kano

Rabiu Kwankwaso ya nemi a kashe masu rusa fastocin Atiku
Source: Depositphotos

A makon nan ne mu ka samu labari cewa Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso yayi jawabi mai kaushi game da yakin neman zaben 2019. Tsohon gwamnan na Kano yayi magana a kan wadanda ke rusa fastocin ‘yan takarar PDP a kano.

Rabiu Kwankwaso yake cewa wasu matasa da ake ba kayan shaye-shaye, sun zo har gaban gidan sa, sun yi fata-fata da alamomin Atiku Abubakar da ya makala. Kwankwaso ya bayyanawa wasu ‘yan jarida wannan ne a gidan sa.

Injiniya Kwankwaso yace wadannan mutane da su ka yi masa irin wannan ta’adi sun taki sa’a cewa ba ya nan, inda yace da a ce yana gida lokacin da aka yi wannan aiki, da ya nemi a dirkawa wadannan mutane dalma a jikinsu.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya kasa daga hannun dan takara a jihar Zamfara

Kwankwaso yace abin da ake yi wa ‘Yan PDP ya fara yawa a Kano inda yake barazanar cewa za su yi maganin duk wanda ya taba su tun daga gwamna mai-ci zuwa kan kowa. Kwankwaso yake cewa su ne ke da Kano ba wasu ba.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kuma kara da cewa ko lokacin da ya zauna a Abuja yayin da yake Sanata, shi ya ga dama. ‘Dan majalisar yake cewa ba su neman kowa da fada, amma za su yi maganin duk wanda ya taba su.

A cikin ‘yan kwanakin nan ne Kwankwaso ya caccaki malaman addini da yace su ke tsoma baki cikin harkar siyasa. Wannan kalamai na tsohon gwamnan dai sun jawo suka daga bakin malaman kasar nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel