Bayan an nemi N10,000,000 an rasa a karkashin kulawarsa, EFCC ta cafko shi yayi bayani

Bayan an nemi N10,000,000 an rasa a karkashin kulawarsa, EFCC ta cafko shi yayi bayani

- EFCC ta cafke tsohon ma'aikacin JAMB

- Ma'akacin ya nemi microfinance bank ya bashi rancen kudi naira miliyan Goma (N10,000,000.00)

-Bincike ya nuna wanda ake tuhumar ya aikata laifuka da dama na cin dukiyar gwamnati

Akalla mutum 30 'yan PDP ne suka rasu a hadurruka daban-daban a yau

Akalla mutum 30 'yan PDP ne suka rasu a hadurruka daban-daban a yau
Source: Depositphotos

EFCC ta cafke wani tsohon ma'aikacin hukumar share fagen shiga jami'a (JAMB) bisa cin kudi N10m.

Hukumar ta EFCC ta samu nasarar cafke Kola Al-amin wanda ya kasance tsohon ma'aikaci ne a hukumar nan ta zana jarrabawar share fagen shiga jami'a (JAMB) a ofishin ta dake jihar Ibadan.

An kama shine saboda wani lokaci a baya a watan Nuwamba shekara ta 2010 Kola wanda ke rike da "Cool Tchnologies Consult limited" wanda ofishin sa ke No 4/900,Taiwo house bene na Biyu a Yemetu total garden a jihar Ibadan inda ya nemi bashi a microfinance bank da sunan hedkwatar JAMB dake Abuja.

Ya nemi Microfinance bank ya bashi rance kudi naira miliyan Goma(10,000,000.00) dan yin kasuwancin LOP.

Ya karbi kudin da yarjejeniyar cewa da sanin JAMB kuma aka tura kudin kai tsaye cikin asusun sa na banki.

GA WANNAN: An zargi Obasanjo da INEC da hada kai don taimakawa PDP da dage zabe

A yayin da lokacin biyan wannan kudi yayi an nemi wanda ake tuhumar sama ko kasa an rasa yayin da hukumar ta JAMB tace wanda ake tuhumar yabar aiki da hukumar tuntuni.

Da aka zurfafa bincike an gano cewa Kola ya aikata laifukan cin kudin gwamnati da dama da sunan shi ma'aikacin JAMB ne.

Za'a mikashi gaban kotu da zarar an gama bincike.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel