CBN ta hana 'yan Jarida kallo yadda ake rarrabe kayan zabe a wasu jihohi

CBN ta hana 'yan Jarida kallo yadda ake rarrabe kayan zabe a wasu jihohi

- An dakatar da manema labarai daga daukar rahoto a yayin da ake maida kayan zabe ma'adanar su

- An gayyaci manema labarai zuwa wajen da abun ya gudana da misalin karfe 10:00am a hedkwatar hukumar zaben

- Bayan sunyi jiran awa Guda cur sai kuma akace su koma bakin aikin su saboda bazasu samu damar daukar rahoton ba

CBN ta hana 'yan Jarida kallo yadda ake rarrabe kayan zabe a wasu jihohi

CBN ta hana 'yan Jarida kallo yadda ake rarrabe kayan zabe a wasu jihohi
Source: Twitter

A jiya ne a Owerri ma'aikatan babban bankin Najeriya (CBN) suka hana manema labarai shiga harabar wajen da ake kokarin maida kayan aikin zabe da aka fitar wanda hukumar zaben takai bankin ajjiya.

CBN ta hana 'yan Jarida kallo yadda ake rarrabe kayan zabe a wasu jihohi

CBN ta hana 'yan Jarida kallo yadda ake rarrabe kayan zabe a wasu jihohi
Source: Twitter

Wadanda babban bankin ya bada umarnin hanawa su shiga wajen sun hada da Charles Ogugbuaja wakilin jaridar nan ta(the guardian) Ndidi Okodili ( The nation) Chinazo Ilechukwu ( FRCN) da kuma Chidi Amadi( Imo state broadcasting corporation).

Shugaban hukumar zaben yankin Prof Francis Chukwuemeka Ozeonu ya gayyaci manema labarai zuwa halatar wajen da misalin karfe 10:00am a hedkwatar hukumar zaben dake kusa da CBN.

GA WANNAN: 'Dage zabe da INEC tayi wani mummunan shiri ne kan mulkin Buhari'

Bayan manema labaran sun halarci wajen kuma sunyi jira na tsayin awa 1 sai sako ya samesu cewa su koma bakin aikin su saboda baza'a basu damar daukar rahoton ba.

Irin hakance ta kasance ga manema labarai a jihar Kebbi bayan sun samu goran gayyata daga REC Ahmed Mahmud.

Wani mutum wanda akafi sani da Mr Ajayi ya bayyana cewa babu shakka wannan lamari ya fito ne daga wajen shugaban ma'aikatan tsaro na bankin (CSO).

A jihar Adamawa kuwa a yaune hukumar zaben ta shirya kwashe kayan aikin zaben daga kananan hukumomin jihar 21 dan adana su.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel