Kotu za ta saurari karan da ke neman a hana Atiku takara bayan zaben Shugaban kasa

Kotu za ta saurari karan da ke neman a hana Atiku takara bayan zaben Shugaban kasa

- Kotu ta shirya sauraran karan dake neman a hana dan takaran shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar takaran shugabancin kasa a ranan Litinin, 25 Fabrairu

- Hakan zai kasance kwanaki biyu bayan gudanar da zaben shugaban kasa da na yan Majalisa

- Kungiyarda ta shigar da kara na son a hana Atiku takara bisa zarge-zargen da ya shafi rashin kasancewarsa dan kasa

Kotu ta shirya sauraran karan dake neman a hana dan takaran shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar takaran shugabancin kasa a ranan Litinin, 25 Fabrairu, kwana biyu bayan zaben kasar.

An tattaro cewa kungiyar Egalitarian Mission for Africa ne suka shigar da karan a babban kotun Tarayya dake Abuja wanda Justis I E Ekwo na kotu na 6 zai saurara.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa kungiyar na son a hana Atiku takara bisa zarge-zargen da ya shafi rashin kasancewarsa dan kasa.

Kotu za ta saurari karan da ke neman a hana Atiku takara bayan zaben Shugaban kasa

Kotu za ta saurari karan da ke neman a hana Atiku takara bayan zaben Shugaban kasa
Source: Facebook

Kungiyanr ta nemi a duba sashi 25 (1) da (2) da 131 (a) na kundin tsarin kasar Najeriya.

An kuma rahoto cewa jam’iyyar PDP, Hukumar zabe na kasa (INEC), da baban lauyan Gwamnatin Tarayya da ministan shari’a na cikin wadanda aka kwafa a takardan kara.

KU KARANTA KUMA: Ranar Asabar ce ranar hisabin jam’iyyar PDP – Inji Ajimobi

A baya Legit.ng ta rahoto cewa ana zargin Sanata Hope Uzodinma wanda ke neman gwamna a jihar Imo a APC da kokarin yi wa ‘dan takarar jam’iyyar hamayya ta PDP watau Atiku Abubakar aiki a zaben bana.

Ba kowa bane yake zargin ‘dan takaran na jihar Imo da yi wa Alhaji Atiku Abubakar aiki face gwamna mai shirin barin gado na jihar, Rochas Okorocha. Okorocha yace ya san irin taron da Hope Uzodinma yake yi da PDP.

Gwamna Okorocha ya fitar da jawabi na musamman inda yace Cif Hope Uzodinma da magoya bayan sa, su na fitowa kuru-kuru su na kira ga jama’a su marawa Atiku Abubakar na PDP baya a madadin shugaba Buhari na APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel