Kar ku kashe barayin akwatunan zabe - Ortom ya gargadi DSS, Rundunar soji da 'yan sanda

Kar ku kashe barayin akwatunan zabe - Ortom ya gargadi DSS, Rundunar soji da 'yan sanda

- Gwamna Samuel Ortom ya gargadi jami'an tsaro da su bijirewa umurnin shugaban kasa Buhari na kashe barawin akwatin zabe

- Ortom ya ce idan har jami'an tsaron suka bi umurnin shugaban kasar to hakan zai janyo hukunci mai matsanani daga kotun ICC

- Ya jaddada cewa a shirye su ke domin zubar da jininsu na karshe ma damar zai haifar da dorewar demokaradiyar kasar

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya gargadi jami'an hukumar tsaro ta fararen kaya (DSS), Rundunar 'yan sanda da rundunar soji da dama sauran jami'an tsaro da su yiwa kawunansu karatun ta-nutsu tare da bijirewa umurnin Buhari na kashe duk wani barawon akwatin zabe a yayin gudanar da zabukan kasar mai zuwa.

Ortom ya ce jami'an tsaro su bi umurnin shugaban kasa Buhari na daukar mummunan mataki akan barayin akwatunan zabe zai kara yawan adadin kisan 'yan Nigeria ba bisa ka'ida ba, yana mai cewa hakan zai janyo hukunci mai matsanani daga kotun hukunta masu aikata laifukan ta'addanci ta kasa-da-kasa (ICC).

Da ya ke jawabi ga manema labarai a ranar Talata a Abuja, gwamnan ya ce ya zama wajibi rundunar soji da sauran jami'an tsaro su bi dokokin da ke zagaye da zabukan, yana mai cewa ba ya goyon bayan satar akwatunan zabe amma bin matakan da doka ta tanadar shi ya fi mai mamakon daukar mataki a hannu.

KARANTA WANNAN: Ko kadan Dogara ba barazana bane ga nasarata a zabe mai zuwa - Gwamnan jihar Bauchi

Kar ku kashe barayin akwatunan zabe - Ortom ya gargadi DSS, Rundunar soji da 'yan sanda

Kar ku kashe barayin akwatunan zabe - Ortom ya gargadi DSS, Rundunar soji da 'yan sanda
Source: UGC

"Ina sane da cewa APC na shirin baiwa sojoji da sauran jami'an tsaro kariya domin goyon ban 'yan APC da gallazawa jam'iyyun hamayya. Ba zamu amince da hakan ba.

"Ya kamata 'yan Nigeria su sani cewa da yawan mu a shirye su ke domin zubar da jininsu na karshe ma damar zai haifar da dorewar demokaradiyar kasar.

"Gwamnatin da aka zabe ta karkashin demokaradiyya na shirin sauyawa zuwa salon mulkin mallaka. Abun takaici ne ace shugaban kasarmu shi ne zai fito yana furucin da suka sabawa dokokin kasa da kuma kara haddasa kashe kashen rayukan 'yan Nigeria da haddasa kazamin rikici a tsakaninsu," cewar Ortom.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel