Ranar Asabar za'a yi jana'izar PDP na har abada - Ajimobi ya bayyana

Ranar Asabar za'a yi jana'izar PDP na har abada - Ajimobi ya bayyana

- A ranar Asabar ne jam'iyar PDP zata girbi abinda ta shuka a cikin shekaru 16

- A ranar duk wani jagora da wani mamba na jam'iyar APC zai goyawa matanen kwarai baya

- 'Yan takarar zasuci gaba da gudanar da kamfe din su har zuwa ranar Alhamis

Ranar Asabar za'a yi jana'izar PDP na har abada - Ajimobi ya bayyana

Ranar Asabar za'a yi jana'izar PDP na har abada - Ajimobi ya bayyana
Source: Depositphotos

Dan takarar neman kujerar sanata a jihar Oyo ta tsakiya gwamna Abiola Ajimobi ya bayyana ranar Asabar a matsayin ranar da jam'iyar PDP zata girbi abinda ta shuka cikin shekaru 16.

Saboda haka ne yayi kira ga duk wasu shuwagabanni da magoya bayan jam'iyar ta APC dasu fito a ranar Asabar su kada kuri'ar su ga shugaban kasa Muhammad Buhari dan ya dora daga inda ya tsaya.

GA WANNAN: Hukumar Kwastam na kan bincike kan harbi da bindiga, bayan sun halbe wani murus

Ajimobi ya halarci taron da National Executive Committee (NEC), watau kwamitin zababbu na jam'iyar APC wanda ya gudana a ranar Litinin a birnin tarayya Abuja inda aka basu damar cigaba da gudanar da kamfe din su.

Gwamnan yace jam'iyar APC tana cikin kwanciyar hankali duba da goyan bayan da ta samu a yayin gudanar da gangamin kamfe dinta a fadin kasar baki daya.

Ya kara da cewa "wannan Asabar din lokaci ne da PDP zata girbi abinda ta shuka cikin shekaru 16 bayan ta kawo nakasu a cikin sha'anin tattalin arzikin kasar sannan ta azurta wadanda suke tare da ita".

"Ranar Asabar ta gabato saboda haka duk wani shugaba da magoyan bayan APC zasu nuna goyan bayansu ga mutane na kwarai."

Daga karshe yayi kira ga masu ruwa da tsaki da su cigaba da gudanar da kamfe dinsu har zuwa ranar Alhamis.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel