Yawa-yawan 'yan Najeriya na ganin tattalin arzikin kasar ya fara farfadowa - inji masu jin ta bakin jama'a

Yawa-yawan 'yan Najeriya na ganin tattalin arzikin kasar ya fara farfadowa - inji masu jin ta bakin jama'a

- 'Yan Najeriya sun yarda cewa tattalin arzikin kasar na habaka

- An gano hakan ne sakamakon Binciken da ma'aikatar kasafin kudi da tsare tsare ta gudanar

- Shirye shiryen gwamnatin tarayyar kasar yana korar talauci a kasar

Yawa-yawan 'yan Najeriya na ganin tattalin arzikin kasar ya fara farfadowa - inji masu jin ta bakin jama'a

Yawa-yawan 'yan Najeriya na ganin tattalin arzikin kasar ya fara farfadowa - inji masu jin ta bakin jama'a
Source: UGC

A ittifaki da PDU tayi ya nuna cewa da yawan yan Najeriya sun yarda da cewa tattalin arziki na habaka.

Kamar yanda binciken ya nuna, kashi 57.3 na yan Najeriya da suka maida martani sun yarda cewa tattalin arzikin kasar nan na cigaba.

Mr Babatunde Osibamowo, babban mai bada shawara shugaban kasa akan kula da dubawa, karkashin ofishin mataimakin shugaban kasa, yace anyi binciken ne don wayar da kai tare da gano yanayin farfado da tattalin arziki kuma anyi shi ne a watanni uku ba farkon 2018.

Amfanin binciken shine ya maida hankali wajen farfado da tattalin arziki da kuma gina tattalin arziki da zai zamo abin gogayya a kasashen duniya.

Bangaren tabbatarwa na ERGP dake ma'aikatar kasafin kudi da tsare tsaren kasar nan ne yayi binciken.

Osibamowo yace an dau yan Najeriya 2000 daga jihohin kasar nan na kowanne jinsi don binciken. Anyi amfani da hanyar sadarwar ta tafi da gidanka.

GA WANNAN: Hukumar Kwastam na kan bincike kan harbi da bindiga, bayan sun halbe wani murus

Yace sakamakon ya nuna cewa kashi 41 na wandanda suka amsa sun taba samun labarin ERGP, kashi 57.3 na wandanda suka amsa sunce tattalin arziki na habaka, kashi 46.7 sun ce tattalin arzikin na samun cigaba a hankali, kashi 8.4 na sunce tattalin arzikin ya habaka sosai sai kuma kashi 62.7 na wadanda suka amsa sunce shirye shiryen gwamnatin na rage talauci.

Mr. Osibamowo, shugaban PDU yace "Gaskiya sakamakon ya bamu mamaki, ballantana inda yan Najeriya suka ce tattalin arziki na habaka. Wannan ya nuna cewa yan Najeriya sun gano cewa muna farfadowa bayan faduwar tattalin arziki da ya same mu a 2014 kuma akwai yuwuwar cigaba da habakan."

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel