Rundunar soji ta gano wani shiri na kai harin cibiyoyin zabe a jihohi 4

Rundunar soji ta gano wani shiri na kai harin cibiyoyin zabe a jihohi 4

- Rundunar sojin Najeriya ta gano wasu shirye-shirye da wasu yan bangan siyasa da aka yo haya ke yi, don kai hare-hare wasu cibiyoyin zabe

- Yan bangan siyasar na shirin kai hari ne a wasu jihohin Niger Delta hudu da ba a bayyana ba

- Kakakin sojin ya bayyana cewa yan daban da ake ganin suna yiwa wasu yan siyasa aiki ne sun mallaki muggan makamai don hargitsa zaben ranar 23 ga watan Fabrairu da kuma na 9 ga watan Maris a wasu yankuna

Rundunar sojin Najeriya a ranar Talata, 19 ga watan Fabrairu ta gano wasu shirye-shirye da wasu yan bangan siyasa da aka yo haya ke yi, don kai hare-hare wasu cibiyoyin zabe a wasu jihohin Niger Delta da ba a bayyana ba.

Kanal Aminu Iliyasu, kakakin rundunar sojin sashi na 6, Port Harcourt ya bayyana hakan a wata sanarwa dauke da sa hannunsa sannan ya aikewa manema labarai a Port Harcourt, jaridar Independent ta ruwaito.

Rundunar soji ta gano wani shiri na kai harin cibiyoyin zabe a jihohi 4

Rundunar soji ta gano wani shiri na kai harin cibiyoyin zabe a jihohi 4
Source: Depositphotos

Kakakin sojin ya bayyana cewa yan daban da ake ganin suna yiwa wasu yan siyasa aiki ne sun mallaki muggan makamai don hargitsa zaben ranar 23 ga watan Fabrairu da kuma na 9 ga watan Maris a wasu yankuna.

A cewarsa, akwai ingantattun bayanai na kwararru da aka gabatarwa hedkwatar sashin inda aka gano shirin wasu yan siyasa a yankin da ked a alaka da makaman da daukar nauyin ta’addancin.

KU KARANTA KUMA: Ranar Asabar ce ranar hisabin jam’iyyar PDP – Inji Ajimobi

Iliyasu a jawabin ya bayyana cewa an rigada a tanadi ayyuka tare da sauran hukumomin tsaro domin gano yan iskan da kuma gano tushen makamansu.

Kakakin sojin ya kuma yaba ma jama’a akan hadin kai da taimakon da suke ba rundunar, inda ya bukaci da su ci gaba da kasancewa masu in doka da zaman lafiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel