Ko kadan Dogara ba barazana bane ga nasarata a zabe mai zuwa - Gwamnan jihar Bauchi

Ko kadan Dogara ba barazana bane ga nasarata a zabe mai zuwa - Gwamnan jihar Bauchi

- Gwamnan jihar Bauchi ya ce kakakin majalisar wakilan tarayya, Yakubu Dogara, ba zai taba zama barazana ga nasararsa a zaben jihar mai zuwa ba

- Gwamnan, wanda ya bayyana Dogara a matsayin wanda ruwa ya ci shi a siyasa biyo bayan zarginsa da ya yi da cewar ya karkatar da kudaden jihar

- Ya ce Dogara ba zai taba zama silar kawo karshen siyasarsa ko nasarar tazarcensa ba

Gwamnan jihar Bauci Muhammed Abubakar ya bugi kirji da cewar kakakin majalisar wakilan tarayya, Yakubu Dogara, ba zai taba zama barazana ga nasararsa a zaben jihar mai zuwa ba.

A ranar Talata, Gwamna Abubakar ya bayyana hakan a Abuja, a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a babbar sakatariyar jam'iyyar APC ta kasa.

Gwamnan, wanda ya bayyana Dogara a matsayin wanda ruwa ya ci shi a siyasa biyo bayan zarginsa da ya yi da cewar ya karkatar da kudaden jihaar, ya yi barazanar cewa zai maka Dogara kotu aka zarginsa da ya yi.

Ya ce Dogara ba zai taba zama silar kawo karshen siyasarsa ko nasarar tazarcensa ba.

KARANTA WANNAN: Furucin Buhari kan kashe masu satar akwatin zabe ya samu goyon bayan Yarabawa

Ko kadan Dogara ba barazana bane ga nasarata a zabe mai zuwa - Gwamnan jihar Bauchi

Ko kadan Dogara ba barazana bane ga nasarata a zabe mai zuwa - Gwamnan jihar Bauchi
Source: Depositphotos

"Ina so mutane su fara sani cewa Dogara ya zo ne daga wani bangare mafi kankanta a jihar Bauchi. Ina takarar kujerar gwamna ne. Ina sane da inda ya fito. Shi mutum ne da ke daf da nutsewa a cikin ruwa.

"Ni ba abokin hamayyarsa bane, Dogara ne neman duk wata hanya domin ya ga ya lalata mun siyasata, sai dai ko a shekarar 2015, shugaban kasa Buhari bai ci zabe a Bogoyo ba, karamar hukumar da Dogara ya fito. Ni kaina ban cin zabe a garin ba. Amma a yau, Muhammadu Buhari shi ne shugaban kasa, ni ne gwamna a jihar.

"Ya kamata mutane su gane cewa Dora na wakiltar mutanen da ba su wuce 80,000 ba. Na ci zabe a 2015 da tazarar sama da kuri'i 300,000. Don haka, ko a nan, za ku fahimci cewa Dogara sam ba zai iya zama barazana ga nasarata a zaben mai zuwa ba."

Dangane da zargin da Dogara ya yi na cewa gwamnatin jihar Bauchi mai ci a yanzu ta karkatar da akalla N400bn, gwamna Abubakar ya ce: "Ku je shafin yanar gizo na ma'akar kudi ku sauke kasafin da ake turawa jihar Bauchi tun daga watan Yunin 2015 har zuwa yanzu. Sannan ku zo ku yi lissafi. Za ku fahimci cewa adadin kasafin da jihar ta samu bai kai N400bn ba."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel