Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun sace basarake a Nasarawa

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun sace basarake a Nasarawa

Rundunar 'yan sanda reshen jihar Nasarawa ta tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga sun sace Yakubu Dauda, dagacin Sabon Gida-Barkin Kogi da ke karamar hukumar Lafia na jihar.

Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, Samaila Usman ne ya tabbatar da afkuwar lamarin yayin hirar da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a ranar Talata a garin Lafia.

Mr Usman ya ce yan bindigan sun sace basaraken ne a misalin karfe daya da minti ashirin da biyar da daren Litinin a gidansa.

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sace basarake a Nasarawa

Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sace basarake a Nasarawa
Source: Twitter

DUBA WANNAN: INEC ba abar amincewa bane - Sanata Akpabio

A cewarsa, 'yan bindigan sun iso gidan basaraken suna harbe-harbe da bindiga kafin daga bisani su kayi awon gaba da shi kuma a halin yanzu ba san inda suka kai shi ba.

"A lokacin da aka sanar da 'yan sanda abinda ya faru, Kwamishinan yan sanda, Bola Longe ya zaiyarci kauyen kuma ya bayar da umurnin a bi sahun 'yan bindigan domin ceto basarajen.

"Tawagar masu neman basaraken sun hada da jami'an yan sanda masu yaki da fashi da makami da mobile force da kuma 'yan kato da gora da kuma mafarauta na garin," inji shi.

Ya ce tuni rundunar ta sake tsaurara matakan tsaro a garin da kuma dukkan hanyoyin da ya hada garin da kauyukan da ke makwabtaka da su kamar Assakio, Obi da Lafia.

Ya ce rundunar ba za tayi kasa a gwiwa ba har sai ta ceto basaraken tare da hukunta wadanda suka aikata mumunan aikin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel