Kashe masu satar akwatin zabe: An samu sabanin ra'ayi tsakanin Buhari da INEC

Kashe masu satar akwatin zabe: An samu sabanin ra'ayi tsakanin Buhari da INEC

- Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce dokar zabe na kasa za ayi amfani da shi wurin hukunta masu satar akwatin zabe da wasu laifukan

- Wannan ya sha ban-ban da kalaman shugaban kasa, Muhammadu Buhari inda ya ce duk wanda ya saci akwatin zabe a bakin ransa

- Shugaban na INEC kuma ya karyata jita-jitar da ake yadawa na cewa jami'an DSS sun kai sumame gidan wani kwamishinan INEC

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya ce za ayi amfani da dokokin zabe ne wurin hukunta wadanda suka aikata laifuka a yayin gudanar da zaben 2019.

Farfesa Yakubu ya yi wannan jawabin ne a ranar Talata a wurin tattara sakamakon zabe na INEC da ke International Conference Centre (ICC) a Abuja yayin da ya ke jawabi ga masu ruwa da tsaki.

Kashe masu satar akwatin zabe: An samu sabanin ra'ayi tsakanin Buhari da INEC

Kashe masu satar akwatin zabe: An samu sabanin ra'ayi tsakanin Buhari da INEC
Source: UGC

DUBA WANNAN: INEC ba abar amincewa bane - Sanata Akpabio

A bangarensa, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya furta cewa duk wani da ya saci akwatin zabe toh ya sani hakan a bakin ransa ya ke. Buhari ya yi wannan jawabin ne a wurin taron jiga-jigan APC a Abuja.

A yayin da ya ke tsokaci a kan kalaman shugaban kasa, Shugaban INEC, Yakubu ya ce za a hukunta wadanda suka saci akwatin zabe na bisa tanadin dokar zabe wato electoral law.

"Matsayar hukumar INEC shine za tayi amfani da dokar zabe wurin hukunta duk wadanda aka samu da hannu wurin aikata laifuka yayin zabe," inji shi.

Kazalika, shugaban na INEC ya musanta cewa jami'an yan sandan farar hula DSS sun kai sumame gidan wani kwamishinan zabe.

"Babu wani kwamishinan zabe da DSS ta kama ko kuma bincike gidansa. A halin yanzu a ranar Talata kwamishinan da ake magana a kai yana ofishinsa da ke hedkwatan INEC yana aiki," inji Yakubu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel