Ranar Asabar ce ranar hisabin jam’iyyar PDP – Inji Ajimobi

Ranar Asabar ce ranar hisabin jam’iyyar PDP – Inji Ajimobi

- Gwamna Abiola Ajimobi, ya bayyana ranar Asabar mai zuwa a matsayin ranar hisabin babbar jam’iyyar adawar kasar, PDP

- Ajimobi yace a ranar ne jam'iytyar za ta girbe abunda ta shuka shekaru 16 da suka gabata na mulkin zalunci

- Ya bukaci magoya bayan APC da su fito kwansu da kwarkwatansu domin zabar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta hanyar duba kokarin da gwamnatinsa tayi a shekaru hudu da ya gabata

Dan takarar kujerar sanata na yankin Oyo ta Kudu a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Gwamna Abiola Ajimobi, ya bayyana ranar Asabar mai zuwa a matsayin ranar hisabin babbar jam’iyyar adawar kasar, Peoples Democratic Party (PDP), domin ta girbe abunda ta shuka shekaru 16 da suka gabata.

Ya kuma bukaci shugabanni da magoya bayan APC da su ci gaba da jajircewa da nuna goyon bayansu ga jam’iyya mai mulki ta hanyar tabbatar da cewa su fito kwansu da kwarkwatansu domin zabar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta hanyar duba kokarin da gwamnatinsa tayi a shekaru hudu da ya gabata.

Ranar Asabar ce ranar hisabin jam’iyyar PDP – Inji Ajimobi

Ranar Asabar ce ranar hisabin jam’iyyar PDP – Inji Ajimobi
Source: Depositphotos

Da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki a sakatariyar jihar a jiya Talata, 18 ga watan Fabrairu, gwamnan yayi gargadi akan tayar da fitina.

Ajimobi wanda ya halarci taron kwamitin masu ruwa da tsaki na APC a Abuja a ranar Litinin, ya bayyana cewa Shugaban jam’iyyar na kasa ya bayar da umurni ga shugabannin jam’iyyar na jihad a su sake karfafa kamfen din jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: ‘Dan takaran APC, Uzodinma yana yi wa Jam’iyyar PDP aiki a zaben 2019 – Okorocha

A wani lamari na daban, mun ji cewa Kungiyar Sunnah ta Najeriya mai suna Sunnah Group of Nigeria (SGN) ta zargi dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar da samun nasaba da kungiyar yan uwa Musulmi na Shi’a.

A wani jawabi da Shugaban kungiyar, Muntaka Kafinsoli, ya ake wa manema labarai a ranar Talata, 19 ga watan Fabrairu yayi zargin cewa dan takarar Shugaban kasar na PDP a yanzu haka yana neman alfarmar kuri’u daga wajen yan Shi’a.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel