Yaki da miyagun kwayoyi: A shirye nake na sadaukar da raina – Kwamishinan Yansandan Kano

Yaki da miyagun kwayoyi: A shirye nake na sadaukar da raina – Kwamishinan Yansandan Kano

Sabon kwamishinan Yansandan jahar Kano, Muhammad Wakili ya bayyana manufarsa ta yaki da sha da ta’ammali da miyagun kwayoyi a jahar Kano, koda kuwa hakan zai yi sanadiyyar salwantar rayuwarsa, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Wakili ya bayyana haka ne a yayin wata ziyarar ban girma da cibiyar yan jaridu ta kai masa a ofishinsa dake garin Kano a ranar Talata, 19 ga watan Feburairu, inda ya bayyana shaye shaye a matsayin ummul haba’isun duk wasu laifuka da ake aikatawa.

KU KARANTA: Kai jama’a: Yan bindigan sun sace dakacin kauye sukutum a jahar Nassarawa

Yaki da miyagun kwayoyi: A shirye nake na sadaukar da raina – Kwamishinan Yansandan Kano

Kwamishinan Yansandan Kano
Source: UGC

“Babu wani yaki da ya wuce yaki da miyagun kwayoyi, saboda yaki ne daya shafi Malamai, matasa da Mata, wannan ziyara taku ta bani kwarin gwiwar cewa har yanzu akwai mutanen kirki a tsakanin al’umma dake bani goyon baya.

“Idan har kuka fahimci ina wuce gona da iri a aikina, don Allah kada ku ji shakkun janyo hankalina, ina tabbatar muku ba zan fasa gyarawa ba, kuma zan umarci duk Yansandan dake sashin watsa labaru dasu yi rajista da wannan cibiya.” Inji shi.

A jawabinsa, jagoran tawagar yan jaridun, Sule Yau Sule ya bayyana cewa dalilin ziyararsu itace domin baiwa kwamishinan kwarin gwiwar cigaba da gudanar da kyakkyawar aikin da yake yi, don haka ya zama wajibi su hada kai da shi domin kawar da matsalar daga jahar Kano.

“A cikin yan kwanaki kalilan da zuwanka ka nuna jajircewa a yaki da miyagun kwayoyi a jahar Kano, muna fatan hakan zai canza rahoton dake bayyana jahar Kano a matsayin jahar dake kan gaba a harkar shaye shaye.

“Muna fatan zaka shugabanci hukumar NDLEA wata rana, zamu cigaba da kokarin ganin ka zama shugaban NDLEA .” Inji shi.

Daga karshe shima shugaban cibiyar NIPR reshen jahar Kano, Aminu Hamza ya bayyana damuwarsa da yadda jahar Kano wanda aka santa da kasancewa cibiyar kasuwanci, sai gashi kuma a yanzu tayi kaurin suna wajen shaye shaye da dabanci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel