‘Dan takaran APC, Uzodinma yana yi wa Jam’iyyar PDP aiki a zaben 2019 – Okorocha

‘Dan takaran APC, Uzodinma yana yi wa Jam’iyyar PDP aiki a zaben 2019 – Okorocha

Mun samu labari cewa ana zargin Sanata Hope Uzodinma wanda ke neman gwamna a jihar Imo a APC da kokarin yi wa ‘dan takarar jam’iyyar hamayya ta PDP watau Atiku Abubakar aiki a zaben bana.

‘Dan takaran APC, Uzodinma yana yi wa Jam’iyyar PDP aiki a zaben 2019 – Okorocha

Okorocha yace Sanata Uzodinma yana tare da Atiku
Source: UGC

Ba kowa bane yake zargin ‘dan takaran na jihar Imo da yi wa Alhaji Atiku Abubakar aiki face gwamna mai shirin barin gado na jihar, Rochas Okorocha. Okorocha yace ya san irin taron da Hope Uzodinma yake yi da PDP.

Gwamna Okorocha ya fitar da jawabi na musamman inda yace Cif Hope Uzodinma da magoya bayan sa, su na fitowa kuru-kuru su na kira ga jama’a su marawa Atiku Abubakar na PDP baya a madadin shugaba Buhari na APC.

KU KARANTA: Atiku ya saduda da zaben 2019 ya san Buhari zai tika sa da kasa

Okorocha yake cewa ‘dan takaran na APC yana kokarin ganin shugaba Muhammadu Buhari da sauran ‘yan takaran jam’iyyar da ke neman kujerun majalisa sun sha kasa a zaben 2019 ta hanyar hada kai da PDP da Atiku Abubakar.

Gwamnan mai shirin barin kan mulki yace Sanatan na APC mai nema ya gaje sa, yana halartar taro da mutanen Atiku Abubakar da nufin ganin an tika jam’iyyar sa ta APC mai mulki da kasa a babban zaben da za ayi cikin kwanakin nan.

Wani babba a jam’iyyar APC da ke tare da Hope Uzodinma ya karyata wannan magana da ake yi. Kwanan nan ne ma dai aka ji Cif Uzodinma yana cewa mutanen kudancin kasar za su zabi Buhari a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel