Zaben 2019: Atiku na da alaka da yan Shi’a – Kungiyar Sunnah

Zaben 2019: Atiku na da alaka da yan Shi’a – Kungiyar Sunnah

Kungiyar Sunnah ta Najeriya mai suna Sunnah Group of Nigeria (SGN) ta zargi dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar da samun nasaba da kungiyar yan uwa Musulmi na Shi’a.

A wani jawabi da Shugaban kungiyar, Muntaka Kafinsoli, ya ake wa manema labarai a ranar Talata, 19 ga watan Fabrairu yayi zargin cewa dan takarar Shugaban kasar na PDP a yanzu haka yana neman alfarmar kuri’u daga wajen yan Shi’a.

Sai dai kungiyar ta gaza gabatar da wani kwakwaran hujja akan zargin da take yiwa tsohon mataimakin Shugaban kasar.

Zaben 2019: Atiku na da alaka da yan Shi’a – Kungiyar Sunnah

Zaben 2019: Atiku na da alaka da yan Shi’a – Kungiyar Sunnah
Source: Twitter

Atiku bai fito karara yayi sharhi akan Shi’a ba tun bayan da ya fara kamfen din shugabancin kasar sa, amma a farkon wannan watar, kungiyar Shi’a ta rubuta wata budaddiyar wasika ga Atiku inda suka yaba masa akan mutunta kundin tsarin mulki.

KU KARANTA KUMA: Atiku ya lissafa jihohin arewa 3 da ake shirin sake daga zabe

Hakan ya biyo bayan karar da Atiku ya kai gaban kasashen, Ingila, Amurka da Birtaniya,inda yayi zargin cewa gwamnatin Muhammadu Buhari na tozarta yancin al’umma.

Daga cikin wadanda aka take wa hakki Atiku ya ambaci Zakzaky da iyalansa duk da umurnin da kotun tarayya ta bayar das akin Shugaban yan Shi’a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel