Zaben 2019: Yakubu Dogara yayi wa Shugaba Buhari wankin babban bargo kan almajirai

Zaben 2019: Yakubu Dogara yayi wa Shugaba Buhari wankin babban bargo kan almajirai

Kakakin majalisar wakilai kuma daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar adawa ta PDP a tarayyar Najeriya, Yakubu Dogara ya soki shugaban kasa Muhammadu Buhari da cewar, tun da ya hau karagar mulki, cikin shekaru 4 babu abunda ya tsinawa almajirai.

Da ya ke magana a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a Abuja, Dogara ya ce Buhari a yanzu ba shi da farin jini saboda yadda ya yi watsi da 'yan Najeriya ciki kuwa hadda almajirai da sauran jama’ar Nijeriya.

Zaben 2019: Yakubu Dogara yayi wa Shugaba Buhari wankin babban bargo kan almajirai

Zaben 2019: Yakubu Dogara yayi wa Shugaba Buhari wankin babban bargo kan almajirai
Source: Depositphotos

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun tafka mummunar ta'asa a jihar Katsina

A cewarshi, “Mun zaci Buhari zai zabi ya zama ministan ilimi ne ba na man fetur ba.” Ya ce babu ruwan Buhari da bangaren ilimi wanda zai tallafawa al’umma.

A wani labarin kuma, Yayin da harkokin siyasa a tarayyar Najeriya ke cigaba da zafafa a kusan dukkan bangarori, Sakataren gudanarwa na jam'iyyar adawa a mataki na tarayya kuma mai mulki a matakin jihar Abia ta PDP Mista Moses Ogbonna ya sanar da murabus din sa.

Mista Ogbonna wanda ya bayyana hakan a cikin wata wasika da ya aikewa shugaban jam'iyyar na jihar Abia Sir Johnson Onuigbon kuma ya ba da kwafin ta ga manema labarai tun ranar Litinin din da ta gabata ya ce va zai iya cigaba da zama dan jam'iyyar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel