Furucin Buhari kan kashe masu satar akwatin zabe ya samu goyon bayan Yarabawa

Furucin Buhari kan kashe masu satar akwatin zabe ya samu goyon bayan Yarabawa

- Wata kungiyar Yarabawa ta goyi bayan Buhari kan tsattsauran matakin da aka dauka ga 'yan Nigeria da ke shirin kawo cikas a zaben kasar

- Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa Buhari, ya yi barazanar cewa duk wasu shirin satar akwatunan zabe to shirya yin hakan a bakin rayuwarsu

- A cewar kungiyar, bayyana matsayarsu tamkar kira ne ga jami'an tsaro dasu kasance masu nuna halin ba-sani-ba-sabo a yayin da suka ci karo da barayin akwati

Wata kungiya da ke fafutukar ganin ci gaban matasan Yarabawa sun goyi bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari kan tsattsauran matakin da aka dauka ga 'yan Nigeria da ke shirin kawo cikas a babban zaben kasar da ke gabatowa.

A ranar Litinin, shugaban kasa Muhammadu Buhari, a wai taron kusoshi da shuwagabannin kungiyoyin jam'iyyar APC da ya gudana a Abuja, ya yi barazanar cewa duk wasu shirin satar akwatunan zabe to shirya yin hakan a bakin rayuwarsu.

Wannan gargadi na shugaban kasar bai yiwa jam'iyyun hamayya dadi ba, wadanda suke kalon cewa shugaban kasar na son yin amfani da karfin iko da kuma bin duk wasu hanyoyi domin ci gaba da kasancewa akan mulkin kasar, ko da kuwa ta hanyar satar akwatunan zabe ne.

KARANTA WANNAN: Babu wani tabbaci na cewar INEC za ta iya gudanar da zabe a ranar 23 ga watan Fabreru

Furucin Buhari kan kashe masu satar akwatin zabe ya samu goyon bayan Yarabawa

Furucin Buhari kan kashe masu satar akwatin zabe ya samu goyon bayan Yarabawa
Source: UGC

Sai dai, kungiyar matasan Yarabawan ta goyi bayan shugaban kasar kan wannan matakin da ya ce kasar za ta dauka. Kamar yadda kungiya ta bayyana a cikin wata sanarwa daa Kola Salawu, shugabanta na kasa, kungiyar ta ce za ta bayar da goyon baya wajen gudanar da sahihin zabe.

A cewar kungiyar, bayyana matsayarsu tamkar kira ne ga jami'an tsaro dasu kasance masu nuna halin ba-sani-ba-sabo a yayin da suka ci karo da barayin akwati, mummunar al'adar da suka ce ta dade tana kawo tangarda a sahihancin zabukan kasar.

Kungiyar PPY ta kara da cewa wadanda hukuncin zai shafa ba za su kasance wadanda basu ji ba basu gani ba, duk wani dan Nigeria na kwarai ba zai saci akwati ba. Inda tayi zargin cewa PDP ta shirya gungun jama'a da nufin satar akwatunan zabe da zarana an kusa kammala zaben.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel