Shika-shikan-faduwa: Kwanaki 3 kafin zabe, Sakataren gudanarwar PDP yayi murabus

Shika-shikan-faduwa: Kwanaki 3 kafin zabe, Sakataren gudanarwar PDP yayi murabus

Yayin da harkokin siyasa a tarayyar Najeriya ke cigaba da zafafa a kusan dukkan bangarori, Sakataren gudanarwa na jam'iyyar adawa a mataki na tarayya kuma mai mulki a matakin jihar Abia ta PDP Mista Moses Ogbonna ya sanar da murabus din sa.

Mista Ogbonna wanda ya bayyana hakan a cikin wata wasika da ya aikewa shugaban jam'iyyar na jihar Abia Sir Johnson Onuigbon kuma ya ba da kwafin ta ga manema labarai tun ranar Litinin din da ta gabata ya ce va zai iya cigaba da zama dan jam'iyyar ba.

Shika-shikan-faduwa: Kwanaki 3 kafin zabe, Sakataren gudanarwar PDP yayi murabus

Shika-shikan-faduwa: Kwanaki 3 kafin zabe, Sakataren gudanarwar PDP yayi murabus
Source: UGC

KU KARANTA: Kalar abinci 5 dake lalata hanta

Legit.ng Hausa ta samu cewa da yake karin haske akan dalilin murabus din nasa, Mista Ogbonna ya ce salon mulkin kama karya marar misali da rashin daratta su shugabannin jam'iyyar ne ya tunzurashi ya dauki matakin.

Ya kara da cewa haka zalika akwai kudaden albashin su da ya kamata a biya su kusan watanni da dama da suka shude amma akayi kunnen uwar shegu da su duk da tuni da suka sha yi akan hakan.

Haka ma Mista Ogbonna ya koka akan yadda yace shugaban jam'iyyar ta PDP a jihar yayi wa sauran masu rike da mukaman jam'iyyar babakere inda ya tauye kowa baya bari su gudanar da ayyukan su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel