Babu wani tabbaci na cewar INEC za ta iya gudanar da zabe a ranar 23 ga watan Fabreru

Babu wani tabbaci na cewar INEC za ta iya gudanar da zabe a ranar 23 ga watan Fabreru

- Kungiyar CCA, ta yi gargadin cewa ba lallai ba ne hukumar INEC ta gudanar da zabe a ranar Asabar 23 ga watan Fabreru kamar yadda ta sanya

- Hukumar ta ce zaben ba zai iya gudana ba saboda gazawar INEC na kammala shirye shirye da kuma rikicin cikin gida tsakanin shuwagabannin hukumar

- Da wanan ne kungiyar CCA ta gargadi hukumar INEC da ta gaggauta kawo dai-daiton lamuran a cikin shugabancin hukumar

Wata kungiya mai zaman kanta, Citizens for Change and Advancement (CCA), ta yi gargadin cewa ba lallai ba ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta gudanar da zabe a ranar Asabar 23 ga watan Fabreru kamar yadda ta sanya, saboda gaza kammala shirye shirye da kuma rikicin cikin gida tsakanin shuwagabannin hukumar.

Daraktan tsare tsare na kungiyar CCA, Maxwell Abaji a cikin wata sanarwa, ya ce har yanzu akwai muhimman kayayyakin zaben wasu jihohi da ke ajiye a ofishin hukumar INEC, ba wai a a ma'adanar babban bankin Nigeria CBN ba, kamar yadda hukumar ta yi ikirari a baya.

"Muhimman kayayyakin zaben wasu jihohi kmar Taraba, Cross River, Ebonyi da Benue ba sa cikin ma'adanar CBN, ikirarin hakan da hukumar INEC ta yi ba gaskiya bane. Su kansu shuwagabannin INEC ba san taka mai-mai inda kayayyakin suke ba har zuwa karfe 4 na yammacin ranar Talata. Lallai abun damuwa ne ace har yanzu wani mai ruwa da tsai a zaben kasar bai tantance wadannan kayayyaki ba," acewar Abaji.

KARANTA WANNAN: Muguwar alakar da ke tsakanin Obasanjo da PDP ce za ta kashe Nigeria - Ameh Ebute

Babu wani tabbaci na cewar INEC za ta iya gudanar da zabe a ranar 23 ga watan Fabreru

Babu wani tabbaci na cewar INEC za ta iya gudanar da zabe a ranar 23 ga watan Fabreru
Source: Depositphotos

Kungiyar ta kuma kara zargin cewa shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu da shugaban sashen gudanar da ayyuka da tsare tsare na hukumar, Farfesa Okechukwu Ibeanu, na ci gaba da boye bayanan tsare tsare daga sauran kwamishinonin hukumar na kasa saboda rikicin cikin gida da rashin iya shugabanci, da kuma rashin jituwa tsakanin shuwagabannin hukumar.

"Duba da rahoton da muka samu, shugaban hukumar INEC da Ibeanu na ci gaba da boye wasu muhimman bayanai ka sauran kwamishinonin hukumar na kasa musamman tsare tsaren zaben ranar Asabar; sun tattara harkokin hukumar da zaben kasar sun barwa junansu kawai, wannan zai sa lallai zaben mai zuwa shima ya samu tangarda.

Da wanan ne kungiyar CCA ta gargadi hukumar INEC da ta gaggauta kawo dai-daiton lamuran a cikin shugabancin hukumar, tana mai cewa 'yan Nigeria ba za su lamunci sake dage zaben kasar ba a kar na biyu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel