2019: Za mu yi maganin masu neman tada kafar-baya inji Jami’an tsaro

2019: Za mu yi maganin masu neman tada kafar-baya inji Jami’an tsaro

- A jiya ne Hafsoshin tsaron Najeriya su ka gana da Shugaban kasa Buhari

- Sufeta Janar na ‘Yan Sanda IG ya bayyana abin da taron na su ya kunsa

- Shugaban ‘Yan Sandan ya gargadi masu shirin tada rikici a zaben na bana

2019: Za mu yi maganin masu neman tada kafar-baya inji Jami’an tsaro

Jami'an tsaro sun ja kunnen masu shirin kawo rigima a zaben 2019
Source: Original

Mun ji labarin yadda taron da manyan hafsun soji da na ‘yan sanda su kayi da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasance jiya. Manyan jami’an tsaron kasar sun ce ba za su bari a kawo wani hargitsi a zaben 2019 ba.

Shugaban kasar ya gana da hafsoshin kasar wanda su ka hada da Janar Gabriel Olonisakin; Laftana Janar Tukur Buratai da Admiral Ibok Ekwe Ibas da kuma Ministan tsaron Najeriya Mansur Dan- Ali mai ritaya a jiya Talata.

KU KARANTA: Mun fara saita na’urorin card readers da za ayi amfani da su - INEC

Shugaban ‘yan sanda na kasa IG Mohammed Adamu yayi jawabi bayan taron a madadin sauran jami’an tsaro na Najeriya. Adamu yace sun bayyanawa shugaban kasar halin da harkar tsaro yake ciki a halin yanzu a Najeriya.

Sufetan yake cewa sun cin ma matsaya cewa za su yi kokarin ganin an yi zabe lafiya ba tare da wani tashin hankali ba. IGP din yake cewa za a ba kowa dama yayi zabe tare da kokarin ganin sun casa masu neman kawo rikici.

Sauran wadanda su ka halarci taron sun hada Air Marshall Abubakar Sadique; Darektan hukuma NIA Ahmed Abubakar; da IGP Mohammed Adamu da shugaban DSS Yusuf Magaji Bichi da kuma NSA Babagana Monguno.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel