Muguwar alakar da ke tsakanin Obasanjo da PDP ce za ta kashe Nigeria - Ameh Ebute

Muguwar alakar da ke tsakanin Obasanjo da PDP ce za ta kashe Nigeria - Ameh Ebute

- Wani tsohon shugaban majalisar dattihjai, Ameh Ebute ya yi ikirarin cewa an kulla wata muguwar dangantaka tsakanin Obasanjo da shuwagabannin PDP

- Sai dai Mr Ebute ya ce wannan alakar ba za ta iya tarwatsa irin nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu a kasar a cikin kasa da shekaru hudu ba

- Ya ce kungiyar CPC ta yi Allah-wadai, da taron dangin da PDP da tsohon shugaban kasar suka yi domin ganin sun tunkude gwamnati mai ci a yanzu

Wani tsohon shugaban majalisar dattihjai, Ameh Ebute ya yi ikirarin cewa an kulla wata muguwar dangantaka tsakanin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da shuwagabannin jam'iyyar PDP.

Ebute ya ce wannan muguwar alakar tsakanin Obasanjo da shuwagabannin jam'iyyar PDP ba zata haifar da d'a mai ido ba, yana mai cewa ba za ta iya tarwatsa irin nasarorin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta samu a kasar a cikin kasa da shekaru hudu ba.

Ebute, wanda shine shugaban kungiyar Congress for Patriotic Citizens (CPC), a wani taron manema labarai a Abuja, ya yi kira ga 'yan Nigeria da su tashi tsaye domin bijirewa duk wasu marasa kishin ci gaban kasar, da suka kware wajen cin hanci da rashawa, domin ceto kasar daga tarwatsewa.

KARANTA WANNAN: Fadar shugaban kasa da APC na shirin tsige shugaban hukumar INEC -Yakubu Dogara

Muguwar alakar da ke tsakanin Obasanjo da PDP ce za ta kashe Nigeria - Ameh Ebute

Muguwar alakar da ke tsakanin Obasanjo da PDP ce za ta kashe Nigeria - Ameh Ebute
Source: UGC

Ya ce: "Mafi yawan sauran shuwagabannin Nigeria tun samuwar 'yanci ba su samu irin wannan damar ba. Tabbas duk wanda a cikinmu ya ke so ya yi korafi akan wani tasgaro da aka samu na ci gaban kasarmu, to alhakin komai na kan Obasanjo. Dalili? Saboda a hannunsa ne shugabancin kasar da ita kanta kasar ta yi dogon suma na rashin ci gaba. Babu wani katabus da ya yi wajen farfado da kasar daga wannan suma."

Ya ce kungiyar CPC ta yi Allah-wadai, da taron dangin da shuwagabannin jam'iyyar PDP da tsohon shugaban kasar suka yi domin ganin sun tunkude gwamnati mai ci a yanzu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel