Yau INEC za ta gama saita na’urorin ta domin gudanar da zaben Shugaban kasa

Yau INEC za ta gama saita na’urorin ta domin gudanar da zaben Shugaban kasa

Mun ji labari cewa hukumar zabe na kasa mai zaman kan-ta na INEC, ta bayyana cewa ta kusa gama aiki a kan na’urorin da ake amfani da su wajen tantance masu kada kuri’a a zabe watau Card Reader.

Yau INEC za ta gama saita na’urorin ta domin gudanar da zaben Shugaban kasa

Takardun zabe da wasu kaya sun fara isowa Jihohin Najeriya
Source: Instagram

Shugaban hukumar INEC na kasa gaba daya watau Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana wannan a lokacin da yake hira da manema labarai jiya Talata a cikin Garin Abuja. Yakubu yace shirin da INEC take yi yayi nisa.

Mahmood Yakubu yake cewa an yi akalla kashi 98% na aikin da ya kamata ayi a kan na’urorin “Card Reader” da ake amfani da su wajen tantance ainihin masu zabe. INEC ta ware wadannan nau’rori fiye da 180, 000 domin zaben.

KU KARANTA: Majalisar Tarayya ta soki umarnin da Buhari ya ba jami'an tsaro a lokacin zabe

Farfesa Yakubu yana sa rai cewa yau dinnan za a kammala duk wani aiki da za ayi wa nau’rorin domin ayi amfani da su a zaben shugaban kasa da za ayi a karshen makon nan. A Ranar Juma’a za a fara shirin bude wasu ofisisohin aikin zaben.

Yakubu ya fadawa ‘yan jarida cewa jigilar kayan zabe ne ya sa aka dakatar da zaben a makon da ya gabata. Yanzu kuwa ana sa rai an ci karfin wannan aiki. Yanzu dai kayan aikin zaben sun fara isa zuwa jihohin kasar nan kafin lokacin.

A Ranar Laraba zuwa Alhamis ne hukumar INEC za ta shiga da kayan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya zuwa kananan hukumomi inda za a jira Ranar zabe domin jama’a su kada kuri’ar su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel