Atiku ya lissafa jihohin arewa 3 da ake shirin sake daga zabe

Atiku ya lissafa jihohin arewa 3 da ake shirin sake daga zabe

Dan takarar neman zama shugaban kasar Najeriya a karkashin inuwar jam’iyyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya yi zargin cewar ana shirin sake daga zabe a jihohin Adamawa, Borno da Kaduna.

A jawabin da mai taimaka ma sa a bangaren yada labarai, Phrank Shuaibu, ya fitar a jiya, Talata, Atiku ya yi zargin cewar za a daga zabe a jihohin ne domin ganin cewar an shirya magudin da zai bawa shugaba Buhari nasara a zaben da za a gudanar,

Ya yi gargadin cewar duk wani yunkuri na daga zabe a wata jiha daidai yak e da magudin zabe, bangar siyasa da yunkurin tayar da rikici da jam’iyyar PDP ba za ta lamunta ba.

Daga cikin abubuwan da su ka kulla a ganawar shugaban kasa da gwamnoni da kuma shugabannin tsaro akwai batun ganin yadda za a daga zabe a jihohin Adamawa, Borno da Kaduna ta hanyar fake wa da dalilan tsaro domin bawa jam’iyyar APC damar aikata magudin idan an zo sake gudanar da zabe a jihohin.

Kalaman shugaban Buhari ga ‘yan Najeriya a kan gudanar da sahihin zabe na adalci za su zama yaudara idan haka ta tabbata,” a cewar Atiku.

Atiku ya lissafa jihohin arewa 3 da ake shirin sake daga zabe

Atiku
Source: Depositphotos

Ya kara da cewa, “wannan makircin da su ke shirya w aba zai hana jam’iyyar PDP bacci ba, saboda ikon tsamo Najeriya daga mulkin kama karya ya na hannun ‘yan kasa ne ba wasu tsirarun gwamnonin APC da ke son Buhari ya zarce a mulki ta kowanne hali ba.

DUBA WANNAN: Dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar adawa ya goyi bayan Buhari

Atiku ya cigaba da cewa, “gudanar da sahihin zabe na gaskiya a 2019 shine abu ma fi cancanta ga jaririyar siyasar Najeriya.”

Wannan ba shine karo na farko da jam’iyyar PDP da dan takarar ta ke zargin cewar ana shirya ma su magudi a zaben shekarar 2019 ba. Sai dai jam’iyyar APC mai mulki ta ce PDP da dan takarar ta na yin wadannan korafe-korafe ne saboda sun san ba za su yi nasara a zabukan da za a gudanar ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel