Kai jama’a: Yan bindigan sun sace dakacin kauye sukutum a jahar Nassarawa

Kai jama’a: Yan bindigan sun sace dakacin kauye sukutum a jahar Nassarawa

Rundunar Yansandan jahar Nassarawa ta tabbatar da sace wani basaraken gargajiya, dakacin kauyen Gida-Bakin Kogi dake cikin karamar hukumar Lafiya ta jahar Nassarawa, Alhaji Yakubu Dauda da ake zargin wasu yan bindiga sun aikata.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito rundunar Yansandan ta tabbatar da haka ne a ranar Talata, 19 ga watan Feburairu ta bakin kaakakinta, Samaila Usman, wanda ya bayyana cewa da misalin karfe 1:25 na daren Litinin yan bindigan suka yi awon gaba da Yakubu daga gidansa.

KU KARANTA: Matsalolin tsaro ba zasu hana gudanar da zaben 2019 ba – Gwamna El-Rufai

A jawabinsa, Kaakaki Samaila ya bayyana cewa da tsakar dare yan bindigan suka far ma gidan dakacin, inda shigarsu keda wuya suka fara harbin bindiga a sama, daga nan suka cimimiyeshi, suka yi awon gaba da shi.

“A yayin da muka samu rahoton lamarin, ba tare da bata lokaci ba kwamishinan Yansandan jahar, Bola Longe ya garzaya kauyen don jajanta ma iyalan dakacin, sa’annan ya umarci jami’an Yansanda dasu tabbata sun cetoshi.

“A yanzu haka hadakan Yansandan kwantar da tarzoma, Yansanda na musamman masu yaki da yan fashi da makami, yan kato da gora da kuma mafarauta sun bazama cikin dajin da ake zargin yan bindigan sun afka, da nufin ceto dakacin.” Inji shi.

Daga karshe kaakakin yace Yansanda sun karfafa tsaro tare da mamaye yankin, da duk wani hanya daya hade da kauyukan dake makwabtaka da kauyen Gida-Bakin Kogi, kamarsu Assakio, Obi da Lafiya, ya kara da cewa ba zasu huta ba har sai sun ceto dakacin.

A wani labarin kuma gungun yan bindiga dauke da muggan makamai sun tashi kauyuka goma sha bakwai, 17, dake cikin kananan hukumomin Rafi da Shiroro na jahar Neja, inda suka kashe akalla mutane biyar, tare da yin garkuwa da mutane Talatin da biyar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel