Sanata Dino Melaye ya bayyana a bainar jama’a bayan tsawon lokaci a taron PDP

Sanata Dino Melaye ya bayyana a bainar jama’a bayan tsawon lokaci a taron PDP

- An ga Sanata Dino Melaye a wajen taron Jam’iyyar PDP da aka yi

- ‘Dan Majalisar yayi kimanin wata guda ba a gan sa cikin Jama’a ba

- A wajen taron na Majalisar NEC ta PDP, Sanatan dai ya soki Buhari

Sanata Dino Melaye ya bayyana a bainar jama’a bayan tsawon lokaci a taron PDP

Sanata Dino Melaye ya halarci taron NEC na PDP da aka yi a Abuja
Source: Twitter

Mun ji cewa Sanatan Kogi ta Yamma watau Dino Melaye ya fito bainar jama’a a karon farko tun watan Junairun shekarar nan. A wancan lokaci, ‘dan majalisar yayi ta faman arba da ‘Yan Sandan Najeriya bisa zargin sa da aka yi da wani laifi.

Dino Melaye ya fito bainar jama’a ne a wajen babban taron PDP da aka shirya a jiya Talata. A wajen taron, Sanata Dino Melaye bai yi kasa a gwiwa ba, inda ya soma da sukar kalaman shugaban kasa Buhari na harbe barayin akwati.

KU KARANTA: Buhari ya dawo da mulkin Soja na cewa a harbe barayin akwati - Dogara

‘Dan majalisar dai yayi kaca-kaca da shugaba Muhammadu Buhari na bada umarni a kashe duk wanda aka samu zai saci akwatin zabe. Sanatan na PDP yace tun ba yau ba shugaban kasar ya saba keta alfaramar tsarin damukaradiyya

Wannan ne dai karon farko da aka ga Sanatan a fili tun watan jiya. Jami’an tsaro su na zargin sa da hannu wajen kashe wani ‘Dan sanda a shekarar bara. Sanatan yayi kaurin suna wajen sukar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kamar yadda mu ka samu labari, shugaban PDP na kasa, Uche Secondus yayi Allah wadai da matakin da shugaba Buhari ya dauka na kashe masu taba akwatin zabe inda yace hakan ya sabawa doka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel