Ci ba biya: Wasu mutane sun tasa Shehu Sani a gaba akan hakkinsu N5m da ya hanasu

Ci ba biya: Wasu mutane sun tasa Shehu Sani a gaba akan hakkinsu N5m da ya hanasu

Wata kamfanin jarida mai suna The NEWS Magazine ta bara, sakamakon bashin naira miliyan biyar da take bin dan majalisa mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani, wanda tace kememe Sanatan ya hanasu hakkinsu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kamfanin ta bayyana haka ne cikin wata wasika data aika ma shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, inda ta nemi ya kwatar mata hakkinta, kudin da tace tun a watan Mari na shekarar 2018 take bin Sanatan.

KU KARANTA: Matsalolin tsaro ba zasu hana gudanar da zaben 2019 ba – Gwamna El-Rufai

A jawabin kamfanin, kamar yadda lauyanta, Umudjoro ya bayyana, yace a watan Oktobar 2017 ne suka yi wata ganawa da wakilin Shehu Sani, kuma na hannun damansa, Kwamared Abubakar Ahmed a ofishinta dake layin Acme, Ikejan jahar Legas.

Inda Sanatan ya basu aikin tallata ayyukan da yayi a mazabarsa, su kuma suka aiwatar da wannan aiki a jaridarsu ta watan Maris na shekarar 2018, inda suka yi amfani da shafuka guda 10 na tsakiyar jaridar wajen tallata ayyukan nasa.

Kamfanin tace ta yi wannan aiki ne akan duk shafi guda daya naira dubu dari biyar (N500,000), ma’ana kenan idan aka hada shafuka goma zasu bada naira miliyan biyar a jimlace, wanda kace zaka biyamu bayan watanni uku da kammala aikin.

Sai dai kamfanin ta bayyana bacin ranta da ace har yanzu bayan watanni goma sha daya Sanatan ya gagara biyansu kudin aikinsu, kuma kaukauce musu yake yi, saboda duk kokarin da suke yi na ganinsa ya ci tura, balle kuma ya biyasu kudinsu.

“Mun yi masa wannan aiki akan bashi ne saboda a tunaninmu shi mutumin kirki ne, mutum mai mutunci, da kyar daraktan kamfanin, Kunle Ajibade ya samu ganinsa a Legas wata rana, inda ya rokeshi ya biya kudin, amma har yanzu sai wala wala yake mana.” Inji kamfanin.

Daga karshe kamfanin ta nemi shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki ya kwatar musu hakkinsu, sa’annan sun shaida ma Shehu Sani cewa zasu shigar dashi gaban kotu domin neman hakkinsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel