EFCC: Kotun Tarayya ta hana a bada umarni a kamo Abdulrasheed Maina

EFCC: Kotun Tarayya ta hana a bada umarni a kamo Abdulrasheed Maina

- Mun ji labari cewa Kotu ta hana a bada umarni a taba Abdulrasheed Maina

- Kotun Tarayya tace damke Abdulrasheed Maina ya sabawa dokar Najeriya

EFCC: Kotun Tarayya ta hana a bada umarni a kamo Abdulrasheed Maina

Kotun Tarayya ba ta ba EFCC dama ta sa a cafke Abdulrasheed Maina ba
Source: Depositphotos

Babban kotun tarayya da ke cikin garin Abuja ta hana hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta nemi a kama Abdulrasheed Maina kamar yadda labari ya zo mana a cikin makon nan.

Kotun tarayyar ta bada wannan umarni ne a Ranar Litinin dinnan. Alkali mai shari’a, Guwa Ogunbanjo, shi ne ya bada wannan hukunci. Wannan hukunci dai bai wa hukumar EFCC dadi ba inda ta shirya daukaka kara.

KU KARANTA: EFCC ta fara da sabuwar farautar Abdulrasheed Maina

Babban Alkali Guwa Ogunbanjo ya fadawa hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin kasa barna cewa ba ta da hurumin da za ta sa a damko mata tsohon shugaban hukumar gyara harkar fansho na Najeriya Rasheed Maina.

Alkalin kotun tarayyar yake cewa taso Alhaji Maina a gaba ya sabawa tsarin mulki kuma an ci mutuncin sa ne a matsayin sa na mai cikakken ‘yancin kasa. Mai shari’a Ogunbanjo yace bada izni a kama bai halatta ba.

Babban Alkalin kotun mai shari’a Guwa Ogunbanjo yayi hukunci ne da sashe na 41 da kuma 42 na dokar shari’ar aikin Najeriya da aka yi wa garambawul watau "Administration of Criminal Justice Act 2015".

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel