Ba zamu sake amincewa da INEC ba - Sanata Akpabio

Ba zamu sake amincewa da INEC ba - Sanata Akpabio

Tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom kuma Sanata mai wakiltan Akwa Ibom na Arewa a majalisar tarayya, Godswill Akpabio ya ce Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta INEC ta rage kima a idon al'umma.

A yayin da ya ke hira da manema labarai a Abuja, Shugaban marasa rinjaye na majalisar ya ce abu mai wahala ga shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya samu goyon bayan al'umma a yanzu.

Ba zamu sake amince da INEC ba kuma - Sanata Akpabio

Ba zamu sake amince da INEC ba kuma - Sanata Akpabio
Source: UGC

DUBA WANNAN: INEC ta aika kayan aikin zaben jihar Kebbi zuwa Kaduna bisa kuskure

Ya ce: "Ka san INEC hukuma ce mai zaman kanta amma wasu daga cikin ma'aikatan hukumar suna bawa wani bangare fifiko. A wasu jihohin kasar nan mun gano cewa akwai wanin hadin gwiwa tsakanin INEC da gwamnatocin jihohin. Misali a jihar Akwa Ibom, mun ga alamun cewa ba za a gudanar da sahihiyar zabe ba domin ba za a yiwa APC adalci ba.

"Za ka iya ganewa duba da yadda INEC ke gudanar da harkokinta a jihar, kamar yadda ta dauki ma'aikatan wucin gadi da sauran ma'aikata a jihar da kuma irin abubuwan da ake fada ma ma'aikatan wucin gadin. Abinda shugaban APC na kasa ya gano a kan jam'iyyar adawa gaskiya ce."

Sai dai duk da hakan, Sanatan ya ce ya yi imanin cewa jam'iyyarsa za tayi nasara a zaben shugabancin kasa da kuma yankin Kudu maso Kudancin da Kudu maso Gabashin Najeriya duk da cewa jam'iyyar PDP tana da karfi a yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel