Kashim Shettima ya bayyana dalilin Boko Haram na kai masa hari

Kashim Shettima ya bayyana dalilin Boko Haram na kai masa hari

- Gwamna Kashim Shettima na jihar Borno ya ce Boko Haram sun kaiwa tawagarsa hari ne domin karin neman suna

- Gwamnan ya ce wannan yunkutrin kashe shi da akayi ba zai sanya ya karaya ba domin mulki ba na rago bane

- Gwamna Shettima ya ce zai sake komawa garin Gamboru Ngala a mako mai zuwa kuma ba zai yi amfani da mota mai garkuwa ba domin a shirye ya ke ya mutu idan ta kama

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima da ya sha da kyar daga harin da 'yan ta'addan Boko Haram suka kai wa tawagarsa ya ce 'yan ta'addan sun kai masa hari ne domin neman suna da karawa kansu kwarin giwa.

Kashim Shettima ya bayyana dalilin Boko Haram na kai masa hari

Kashim Shettima ya bayyana dalilin Boko Haram na kai masa hari
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Adam Zango ya yi karin haske a kan kai masa farmaki saboda zagin Buhari

A hirar da ya yi da manema labarai a gidan gwamnatin bayan taron masu ruwa da tsaki da ya yi da shugaba Muhammadu Buhari, ya ce duk da cewa ya yi girgiza da yunkurin kashe shi da akayi, ya ce ba za fasa ziyarar al'ummarsa ba domin ba su kwarin gwiwa.

A dai kwanakin nan ne wasu mayakan Boko Haram suka kai wa tawagar Shettima Farmaki a hanyar Maiduguri zuwa Gamboru a hanyarsa ta zuwa yakin neman zabe na takarar kujerar sanata a karkashin jam'iyyar APC.

Ya ce: "Boko Haram neman suna suke so a kullum. Harin da suka kai wa tawaga ta na neman suna ne ba bawa kansu kwarin gwiwa.

"Amma kamar yadda ake cewa shugabanci ba na rago bane. Zan sake komawa Gamboru Ngala mako mai zuwa kuma a shirye nake in rasa rai na kuma ba zan tafi da mota mai garkuwa ba. Zan shiga irin motar da dukkan masu bani tsaro suka shiga.

"Amma ku sani cewa komin duhun dare, gari zai waye. Ba zamu cigaba da kasancewa cikin wannan halin har abada ba.

"Wannan yaki ne tsakanin haske da duhu, tsakanin karya da gaskiya."

Gwamnan ya ce duk da irin hare-haren da 'yan ta'addan ke kaiwa wasu sassan jihar, ba za a taba kwatantawa da halin da jihar ke ciki a baya ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel