Hukumar INEC zata raba kayan aikin zabe a jihar Kano ranar Laraba

Hukumar INEC zata raba kayan aikin zabe a jihar Kano ranar Laraba

Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) reshen jihar Kano ta sanar da cewa za ta fara rabon kayayyakin aikin zabe a dukkan kananan hukumomi 44 dake fadin jihar a ranar Laraba mai zuwa.

Kwamishinan zabe na jihar, Riskuwa Arab-Shehu ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Talata, 19 ga watan Fabrairu Kano.

Ya bayyana cewa: “mun fara rarraba wasu daga cikin kayan zaben kafin a sanar da dage zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dattawa, ina son sanar da ku cewa mun karbi dukkan kayan aikin da muka bukata dan gudanar da zabe a ranar Asabar. “

Hukumar INEC zata raba kayan aikin zabe a jihar Kano ranar Laraba

Hukumar INEC zata raba kayan aikin zabe a jihar Kano ranar Laraba
Source: UGC

Arab- Shehu ya kara da cewa hukumar shiyar jihar Kano ta kammala daidaita na’urar tantancewa sannan ta kamala shirye shiryen yadda zatayi jigilar kayayyakin, zamu fara diban kayayyakin daga babban bankin Nijeriya zuwa ofisoshin INEC da ke kananan hukumomin jihar daga Laraba 20 ga Fabrairu zuwa Alhamis 21 ga Fabrairu.

KU KARANTA KUMA: INEC ta aika kayan aikin zaben jihar Kebbi zuwa Kaduna bisa kuskure

Ya ci gaba da cewa: “mun dauki ma’aikata 41,552 , mun nasu horo sannan mun rarraba su zuwa idan wasu yi aiki tun kafin a dage zaben.”

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga yan Najeriya da kada su yanke tsammani da tsarin zaben kasar sannan ya bukaci masu zabe da su fito su jefa kuri’u a zaben Shugaban kasa da na majalisar dokoki da aka dage.

Shugaba Buhari ya yaba ma yan Najeriya akan hakurinsu da kuma alkawarin yin zabe na gaskiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel