Yanzu Yanzu: PDP ta zargi fadar Shugaban kasa da amincewa da N6bn don magudin zabe

Yanzu Yanzu: PDP ta zargi fadar Shugaban kasa da amincewa da N6bn don magudin zabe

- Jam'iyyar PDP ta zargi fadar Shugaban kasa da amincewa da N6bn don magudin zabe

- PDP tace kowani dan takarar kujerar sanata na APC 109 ya samu naira miliyan 20, yan takarar kujerar majalisar wakilai na APC 360 kuma sun samu naira miliyan 10 kowanni mutum guda

- Jam’iyyar ta PDP tace APC na amfani da kudaden sata don shirya jami’an tsaro na bogi, yan daba da kuma ba jami’an INEC cin hanci domin su yi murdiya a zaben yan majalisa a fadin kasar

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta zargi fadar Shugaban kasa da sakar ma yan takarar kujerar majalisar dokokin kasar na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sama da naira biliyan N6 na kudaden sata daga kudaden tarayya domin jam’iyyar ta samu damar gudanar da shirinta na magudi a zaben da za a gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu.

Daraktan labarai na kungiyar kamfen din PDP, Mista Kola Ologbodiyan ya bayyana a wata sanarwa da yayi a ranar Talata cewa “kowani dan takarar kujerar sanata na APC 109 ya samu naira miliyan 20, yan takarar kujerar majalisar wakilai na APC 360 kuma sun samu naira miliyan 10 kowanni mutum guda, yayinda fadar shugaba Buhari ta raaba kudade daban-daban ga shugabannin APC domin shirin magudi.”

Yanzu Yanzu: PDP ta zargi fadar Shugaban kasa da amincewa da N6bn don magudin zabe

Yanzu Yanzu: PDP ta zargi fadar Shugaban kasa da amincewa da N6bn don magudin zabe
Source: Depositphotos

Jam’iyyar ta PDP tace APC na amfani da kudaden sata don shirya jami’an tsaro na bogi, yan daba da kuma ba jami’an INEC cin hanci domin su yi murdiya a zaben yan majalisa a fadin kasar.

KU KARANTA KUMA: Kuri’unku za su yi amfani – Buhari ya sake jawabi ga yan Najeriya (bidiyo)

Jam’iyyar ta kara da cewa an tattara wasu daga cikin kudaden ne ta hanyar karkatar da kudaden da ya kamata a tallafawa yan gudun hijira a jihohin tarayya daban-daban.

Jam’iyyar ta kara da cewa sauran wuraren da aka samo kuydaden sun hada da kudaden shiga na hukumomi kamar irinsu hukumar Inshoran lafiya ta kasa (NHIS) da hukumar ci gaban Niger Delta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel