APC za ta yi magudi cikin yankuna 3 na Najeriya a babban zabe - Atiku

APC za ta yi magudi cikin yankuna 3 na Najeriya a babban zabe - Atiku

- Atiku ya yi ikirarin cewa jam'iyya mai ci ta APC na shirye-shiryen tafka magudin zabe cikin wasu yankuna uku na kasar nan

- Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ya ce APC ta horas da wasu kwararru a kasar Sin domin aiwatar da aikin murdiya a zaben bana

- Atiku ya ce jam'iyya mai ci ta daura damarar gaggauta gudanar zabe a yankunan da ta ke sa ran samun nasara

Dan takarar kujerar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya yi zargi da cewar jam'iyya mai ci ta APC ta daura duk wata damara ta tafka magudi a yayin babban zaben kasa domin rinjayar da nasara a kanta.

Atiku wanda ya kasance tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya ya bayyana cewa, jam'iyya mai ci ta APC ta daura damarar tafka magudi a yayin babban zaben kasa ta hanyar ribatar na'urarar tantance masu kada kuri'a wajen kulla dabaru na ha'inci.

APC za ta yi magudi cikin yankuna 3 na Najeriya a babban zabe - Atiku

APC za ta yi magudi cikin yankuna 3 na Najeriya a babban zabe - Atiku
Source: Twitter

Kamar yadda kafar watsa labarai ta Sahara Reporters ta ruwaito, Atiku ya yi ikirarin hakan ne a yau Talata yayin taron jiga-jigan jam'iyyar sa ta PDP da aka gudanar a hedikwatar ta da ke babban birnin kasar nan na tarayya.

Atiku ya yi ikirarin cewa, tuni jam'iyya mai ci ta APC ta mallaki wasu na'urorin zamani na daban domin gaggauta gudanar da zabe cikin wasu yankunan kasar nan da ta ke hasashen samun nasara yayin da za ta kawo jinkiri gami da haifar da nawa a yankunan da ba za ta yi nasara ba.

Wazirin Adamawa ya yi zargin cewa, jam'iyyar APC ta horas da wasu kwararrun ma'aikata a kasar Sin da tuni su ka dawowa kasar nan ta Najeriya domin ribatar kwazon su wajen tabbatar da cikar burin ta yayin babban zaben kasa.

KARANTA KUMA: Osinbajo ya daura damarar warware rikicin APC a jihar Zamfara

Cikin jerin yankunan kasar nan da jam'iyyar APC za ta kawo jinkiri tare da haifar da nawa yayin gudanar zabe kamar yadda Atiku ya wassafa sun hadar da; Kudu maso Kudu, Kudu maso Gabas da kuma Arewa ta Tsakiya.

Sauran yankunan uku da jam'iyyar APC za ta gaggauta gudanar zaben domin samun yalwa ta fuskar yawan adadi na masu kada kuri'u sun hadar da yankin Arewa ta Gabas, Arewa da Yamma da kuma Kudu maso Yamma.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel