Motar kayan aikin zaben jihar Zamfara ta yi hatsari

Motar kayan aikin zaben jihar Zamfara ta yi hatsari

Jami’an rundunar ‘yan sanda sun tare motoci biyu da ke dauke da kayan zaben jihar Zamfara da yammacin yau, Talata.

Daya daga cikin motocin kuma ta yi hatsari bayan ta yi karo da wasu Babura guda biyu a kan titin zuwa Sokoto yayin da jami’an ‘yan sanda su ka kama daya motar a daf da Faru, wani gari da ke kan iyakar jihar Sokoto da Zamfara.

Sai dai, kwamishinan ‘yan sanda a jihar Zamfara, Celestine Okoye, da kwamishinan hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC), Hajiya Asma’u Maikudi, da kuma darektan hukumar tsaron farin kaya (DSS) sun shaida wa manema labarai cewar kayan aikin zaben ba su ne ma fi muhimmanci ba. Sun sanar da hakan ne a wani taron hadin gwuiwa da manema labarai a garin Gusau.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: 'Yan Boko Haram sun yanka ma su sana'ar gawayi 18 a Borno

Motar kayan aikin zaben jihar Zamfara ta yi hatsari

Motar kayan aikin zaben jihar Zamfara ta yi hatsari
Source: Twitter

A cewar Maikudi, jami’an ‘yan sanda sun kama kayan aikin zaben ne a hanyar kawo su ofishin INEC.

Sannan ta kara da cewa motar na dauke ne da littafin sunayen ma su zabe da dan kwangila ya sa ka a motar bayan motar da ya fara dauko kayan da ita ta lalace a hanya. Lamarin da ta ce ya tilasta dan kwangilar yin amfani da motoci biyu domin isar da kayan zuwa ofishin INEC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel