Kuri’unku za su yi amfani – Buhari ya sake jawabi ga yan Najeriya (bidiyo)

Kuri’unku za su yi amfani – Buhari ya sake jawabi ga yan Najeriya (bidiyo)

- Shugaban kasa Buhari da su fito su kada kuri'u a zabe mai zuwa

- Buhari ya nuna alhini ga wadanda suka yi tafiyar kilomita da dama domin yin zabe kafin a dage a zaben

- Shugaban kasar ya jadadda cewa za a gudanar da zabe na gaskiya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga yan Najeriya da kada su yanke tsammani da tsarin zaben kasar sannan ya bukaci masu zabe da su fito su jefa kuri’u a zaben Shugaban kasa da na majalisar dokoki da aka dage.

A wani jawabin bidiyo da yayi a ranar Talata, 19 ga watan Fabrairu, Shugaban kasar ya nuna alhini ga wadanda suka yi tafiyar kilomita da dama domin yin zabe kafin a dage a zaben.

Shugaba Buhari ya yaba ma yan Najeriya akan hakurinsu da kuma alkawarin yin zabe na gaskiya.

A ranar Asabar ta makon da ya gabata, 16 ga watan Fabrairun 2019, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta dage babban zaben kasa na kujerar shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya zuwa ranar Asabar ta wannan mako.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: 'Yan Boko Haram sun yanka ma su sana'ar gawayi 18 a Borno

Mun samu cewa daya daga cikin 'yan majalisar tarayya na kasar Amurka, Chris Smith, ya yi tsokaci tare da bayyana ra'ayin sa dangane da dage babban zaben kasar nan na Najeriya a ranar Asabar, 16, ga watan Fabrairun 2019.

Chris Smith, dan majalisar tarayya na kasar Amurka ya ce dage babban zaben kasar nan ta Najeriya ba laifin wani bane face na shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da makarraban sa da kuma makusanta.

Mista Smith, ya ce dole ne shugaban kasa Buhari ya dauki nauyi tare da rataya laifin dage babban zaben kasar nan a wuyan sa kasancewar shugaba kuma mai rike da akalar jagoranci na tafiyar da al'amurran kasar sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel