Yanzu-yanzu: 'Yan Boko Haram sun yanka ma su sana'ar gawayi 18 a Borno

Yanzu-yanzu: 'Yan Boko Haram sun yanka ma su sana'ar gawayi 18 a Borno

A kalla mutane 18 masu sarar itace da masu neman gawayi ne mayakan kungiyar Boko Haram suka yiwa yankan rago a Koshebe da ke karamar hukumar Jere na jihar Borno kamar yadda Sahara Reporters ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin a yayin da mazauna kauyen suka shiga daji domin saro itace da neman gawayi domin sayarwa a garin Maiduguri amma kwatsam sai 'yan ta'adan suka yi musu kwantar bauna suka kama su.

Wata majiya daga jami'an tsaro da ta taimaka wurin kwashe gawarwakin mutanen ta tabbatarwa majiyar Legit.ng cewa a halin yanzu an kwashe gawarwaki 16 zuwa garin Maiduguri.

DUBA WANNAN: An kone motocin INEC dauke kayan zabe a jihar Akwa Ibom, hotuna

Yanzu-yanzu: 'Yan Boko Haram sun yanka ma su sana'ar gawayi 18 a Borno

Yanzu-yanzu: 'Yan Boko Haram sun yanka ma su sana'ar gawayi 18 a Borno
Source: UGC

"Da farko, mun kwashe gawarwakin mutane 10 daga inda Boko Haram suka kai hari a Maiduguri amma zamu koma gobe mu kashe sauran gawarwakin," inji shi.

Ya ce jami'an tsaro kawai aka sanya aikin kwashe gawawarkin a Kadamari a ranar Laraba.

"Yan Boko Haram sun yiwa wasu masu sarar itace kawanya a Koshebe da ke karamar hukumar Jere a yayin da suka shiga daji neman itace," inji wani majiyar.

"Mun ga gawarwaki 18 a wurin da akayi harin amma a halin yanzu gawarwaki 10 kawai jami'an tsaro da Civilian JTF suka kwashe."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel