INEC ta saki nata matsayin kan masu wawason kayan zabe, sai dai ba yadda Buhari yace ba

INEC ta saki nata matsayin kan masu wawason kayan zabe, sai dai ba yadda Buhari yace ba

- An samu bambancin hukunci tsakanin ciyaman na INEC da shugaban kasa Muhammad Buhari akan wanda aka kama da laifin satar akwatin zabe

- Buhari yace jami'an tsaro da soji zasu hukunta duk wanda aka kama da wannan laifi

- A daya bangaren kuma ciyaman ba INEC yace hukumar zabe itake da ikon hukunta duk wanda aka samu da laifin satar akwatin zabe

INEC ta saki nata matsayin kan masu wawason kayan zabe, sai dai ba yadda Buhari yace ba

INEC ta saki nata matsayin kan masu wawason kayan zabe, sai dai ba yadda Buhari yace ba
Source: Depositphotos

A ranar Talata ne ciyaman na hukumar zabe ta kasa (INEC) a sabon tsarin gudanar da zabe ya bayyana cewa "duk wanda aka kama da laifin satar akwatin zabe to fa zai fuskanci hukuncin hukumar wanda doka ta tanada".

An dai yi wa shugaba Buhari caa kan yadda yace a kashe masu son tada zaune tsaye nan take, maimakon yace a kama su. A wasu wuraren ma, har tuni ake masa da yadda shi yayi juyin mulki ya baras da gwamnatin dimokuradiyya gaba-daya a 1983.

Duk da cewa shugaban kasa Muhammad Buhari ya baya jami'an tsaro da soji damar hukunta wanda duk aka samu da aikata wannan laifi.

Da yake magana a yayin gudanar da wani taro na jam'iyar APC a Abuja a ranar Litinin shugaban kasar yace duk wanda aka kama da laifin satar akwatin zabe ba shakka shine aikin sa na karshe akan taka doka.

GA WANNAN: Bani da masaniyar za'a dage zabe, shugaba Buhari ga masu zargin ko shi yasa a dage

"A fadin jihohi 36 na Najeriya nasan ina da magoya baya da dama saboda haka ina can kunnen duk wani wanda ya shirya jagorantar gungun yan daba akan su sace akwatin zabe da kuma kawo tasgado a yayin kada kuri'a ba shakka yayi a bakacin rayuwar sa".

A ranar Talata ne ciyaman na hukumar zabe Prof Mahmood Yakubu ya fitar da nasa jawabin inda yace "hukumar zabe zata hukunta duk wanda aka kama da laifin satar akwatin zabe bisa hukuncin da hukumar ta tanadarwa masu irin wannan laifi".

A doka dai, shugaban kasa bashi da iko yayi aikin da doka ta baiwa INEC damar yi, sai dai hadiman shugaban sunce yada da damar kawar da tada zaune tsaye.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel