Satar Akwati: Kada ku bi umurnin Buhari - Atiku ya yi kira ga Sojoji

Satar Akwati: Kada ku bi umurnin Buhari - Atiku ya yi kira ga Sojoji

Dan takaran kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari da kama karya ne ba dan demokradiyya ba.

Ya ce ba wajibi bane jami'an sojojin Najeriya subi umurnin shugaban kasa ba muddin sun sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Yayinda yake magana a taron gaggawan shugabannin PDP a ranan Talata, Atiku ya ce Buhari bai cikin wadanda su kayi gwagwarmayan demokradiyya a Najeriya.

Yace:"Ina mika sako na ga hafsoshin soji da kwamandoji. Kun san jami'an soji da kwamandoji bai wajaba a kansu su bi umurnin da ya sabawa doka ba."

"Wannan shien doka, wannan shine sunnar gidan soja; saboda haka idan kai kwararren hafsa ne ko soja ko dan sanda, bai wajaba kabi umurnin da ya sabawa doka ba komin wanda ya bada umurnin."

A ranan Litinin, shugaba Muhammadu Buhari ya umurci jami'an sojin Najeriya da yan sanda cewa kada su dagawa suk wanda yayi niyyar tayar da tarzoma kafa. Kuma wanda ya ke yunkurin sace akwatin zabe, to a bakin ransa.

KU KARANTA: Ta kan N20,000 kudin beli, wani matashi ya mutu a hannun yan sanda

Bayan hakan, hukumar sojin Najeriya ta bayyana cewa zata bi umurnin shugaba Buhari. Kakakin hukumar soji, Sagir Musa yace:

"Duk abinda za muyi, bisa ga dokar hukuma ne kuma kundin tsarin mulkin Najeriya."

Za'a yi zabe ranan 23 ga watan Febrairu da 9 ga watan Maris, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel