Dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar adawa ya goyi bayan Buhari

Dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar adawa ya goyi bayan Buhari

Dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin inuwar jam’iyyar APDA, Alhaji Mohammed Abacha, ya bayyana goyon bayan sa ga takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Mohammed, babban dan marigayi tsohon shugaban kasa a mulkin soji, janar Sani Abacha, ya shaidawa manema labarai a ofishin yakin neman zaben sa da ke kan titin Magwan a birnin Kano, cewar zai samar wa shugaba Buhari a kalla kuri’u miliyan biyu a jihar Kano.

Da ya ke bayyana dalilin da ya sa ya zabi ya goyi bayan Buhari a kan ragowar ‘yan takarar shugaban kasa, Mohammed, wanda shugaban jam’iyyar APDA a jihar Kano, Alhaji Bashir Bataya, ya wakilta, ya ce irin nasarorin shugaba Buhari ya samu tun bayan hawan sa mulki ne su ka shi goya ma sa baya.

Dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar adawa ya goyi bayan Buhari

Mohammed Abacha
Source: Getty Images

Mohammed ya taba neman tsohuwar jam’iyyar CPC ta tsayar da shi takarar gwamnan jihar Kano a shearar 2011 amma sai uwar jam’iyyar ta bawa Kanal Jafaru Isa (mai ritaya) tuta.

DUBA WANNAN: Satar akwati: Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin damuwar PDP

Akwai kyakyawar alaka tsakanin shugaba Buhari da marigayi janar Sani Abacha.

Sai dai, wasu na ganin cewar Buhari ya gaza taimakon Mohammed ya samu takarar gwamnan jihar Kano a karkashin tutar tsohuwar jam’iyyar APC a shekarar 2011.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel