Allah ya riga ya zabi Atiku a matsayin Shugaban kasa na gaba – Prophet Udoka

Allah ya riga ya zabi Atiku a matsayin Shugaban kasa na gaba – Prophet Udoka

- Wani babban malamin addini, Prophet Okechukwu Daniel Udoka, ya yi hasashen cewa dan takarar shugban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Aubakar zai kayar da shugaba Buhari

- Malamin yace Allah ya zabi Atiku domin ya zama Shugaban kasar Najeriya na gaba

- Prophet Udoka yayi ikirarin cewa Allah ya fada masa cewa babu abunda zai hana Atiku zama Shugaban kasa na gaba

Wani babban malamin addini, Prophet Okechukwu Daniel Udoka, ya yi hasashen cewa dan takarar shugban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Aubakar zai kayar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a babban zaben kasar.

Allah ya riga ya zabi Atiku a matsayin Shugaban kasa na gaba – Prophet Udoka

Allah ya riga ya zabi Atiku a matsayin Shugaban kasa na gaba – Prophet Udoka
Source: Depositphotos

Malamin yace Allah ya zabi Atiku domin ya zama Shugaban kasar Najeriya na gaba, inda yace dan takarar na PDP ba tsarkakakke bane amma cewa mulkinsa zai fi gwamnatoci hudu da suka gabata a baya.

Prophet Udoka yayi ikirarin cewa Allah ya fada masa cewa babu abunda zai hana Atiku zama Shugaban kasa na gaba, inda yace yan Najeriya da yawa za su zabi Atiku a zabe mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Tsarin Buhari ne ya kori masu zuba hannun jari a Najeriya – Buba Galadima

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Dan takarar Shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari dan kama-karya ne.

Atiku ya bayyana hakan ne a wajen taron da jam'iyyar PDP ta gudanar a Abuja ranar Talata. Sai dai Shugaba Buhari da jam'iyyarsa ta APC ba su ce komai ba kan wannan zargi ba tukuna.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi zargin cewa jam'iyyar APC ta tura wasu mutane kasar China inda suka samu horo kan yadda za su hana na'urar Card Reader "yin sauri" a yankuna da PDP ke da magoya baya da yawa, sannan a sa "na'urar ta yi sauri "a bangarorin da APC ke da magoya baya da yawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel