Kashe-kashen Kaduna: Kungiyar Fulani da yiwa mambobinta gargadi kan ramuwar gayya

Kashe-kashen Kaduna: Kungiyar Fulani da yiwa mambobinta gargadi kan ramuwar gayya

Kungiyar 'yan kabilar Fulani na Gan Allah Fulani Development Association of Nigeria (GAFDAN) ta yi kira ga mambobinta kada su dauki doka a hannunsu game da kisan kiyashin da aka yiwa 'yan uwansu a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

A wata sanarwa da ta fito daga sakataren kungiyar na kasa, Ibrahim Abdullahi a ranar Litinin ya Kaduna, ya yi kira ga mambobin kungiyar su bari gwamnati da hukumomin tsaro su dauki mataki a kan lamarin.

Abdullahi ya ce GAFDAN ta kira taron gaggawa domin tattaunawa a kan kashe mutane fiye da 100 da ake zargin 'Yan Adara ne suka aikata a kauyukan Iri da Maro a ranar 11 ga watan Fabrairu.

Kashe-kashen Kaduna: Kungiyar Fulani da yiwa mambobinta gargadi

Kashe-kashen Kaduna: Kungiyar Fulani da yiwa mambobinta gargadi
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Adam Zango ya yi karin haske a kan kai masa farmaki saboda zagin Buhari

Ya koka a kan yadda al'ummar garin na Adara suka musanta afkuwar lamarin duk da cewa mutane daga ciki da wajen jihar suna musu jaje tare da mika ta'aziyya.

"Muna kira ga mambobinmu su kame kansa daga daukan doka a hannunsu, su bari gwamnati da hukumomin tsaro su dauki mataki.

"Muna kira da gwamnati da hukumomin tsaro su tabbatar cewa wadanda suka aikata wannan laifukan sun fuskanci shar'ia.

"Muna godiya ga gwamna Nasir El-Rufai da sauran hukumomin tsaro da suka ziyarci garuruwan domin gane ma idanunsu abinda ya faru na kisar mutane da asarar dukiyoyi da wadansu miyagu su kayi," inji shi.

Sakataren ya ce kungiyar za ta cigaba da aiki da masu ruwa da tsaki da sauran al'ummar jihar Kaduna masu son zaman lafiya domin ganin an dai-daita tsakanin al'ummar jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel