Tsarin Buhari ne ya kori masu zuba hannun jari a Najeriya – Buba Galadima

Tsarin Buhari ne ya kori masu zuba hannun jari a Najeriya – Buba Galadima

Daya daga cikin jiga-jigan Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Buba Galadima, ya yi zargin cewa, Najeriya ta fada halin komadewar tattalin arziki ne a sakamakon yadda Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsoratar da masu zuba jari, suka gudu suka bar kasar nan.

Galadima ya kuma bayyana cewa, dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, zai iya gyara tattalin arzikin kasar nan, ya fitar da shi daga halin koma baya da yake a cikinsa.

Ya ce, “Sam ban yarda da yanda wannan gwamnatin take ta kokarin kare kanta ba, na cewa wai mun tsinci kanmu ne a cikin komadar tattalin arziki sabili da wai wani ne ya yi facaka da tattalin arzikin namu.

Tsarin Buhari ne ya kori masu zuba hannun jari a Najeriya – Buba Galadima

Tsarin Buhari ne ya kori masu zuba hannun jari a Najeriya – Buba Galadima
Source: Facebook

“Gaskiyan magane ita ce, yanda ya rika nunawa ne da kalaman da ya rika furtawa, suka firgita masu zuba jarin daga waje, inda nan take suka fara janye jarukansu daga kasuwannin kasar nan.

“Suka yi ta hanzarin guduwa, ta yanda ba su damu da su sayi dalar Amurka ba ko nawa ne. wannan shi ne ya jefa mu a cikin komadar tattalin arziki.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: A China APC ta koyo magudin da za ta yi da na'urar tantance ma su zabe - Atiku

Galadima, wanda daya ne daga cikin masu magana da yawun kwamitin kamfen na dan takaran shugaban kasa a inuwar Jam’iyyar PDP, ya fadi hakan ne a ranar Juma’a, a Abuja, lokacin kaddamar da wani Littafi mai taken, “Atikunomics – The Economic Pillar for a New Nigeria,” wanda wani dan jarida mai suna, Bictor Emeruwa, ya rubuta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel