Fadar shugaban kasa da APC na shirin tsige shugaban hukumar INEC -Yakubu Dogara

Fadar shugaban kasa da APC na shirin tsige shugaban hukumar INEC -Yakubu Dogara

- Hon. Yakubu Dogara ya zargi fadar shugaban kasa da jam'iyyar APC, na kulla makircin kunyata INEC, ta hanyar tunbuke Farfesa Mahmood Yakubu daga ofishinsa

- Ya kuma yi tsokaci kan furucin Buhari na cewar duk masu kudurin satar akwatunan zabe su shirya yin hakan a bakin rayuwarsu

- Dogara ya kuma ce sun gano cewa fadar shugaban kasa da APC na matsin lamba ga INEC akan ta gudanar da zabe a wasu jihohi ta kyale wasu

Kakakin majalisar wakilan tarayya, Hon. Yakubu Dogara ya zargi fadar shugaban kasa da jam'iyyar APC, na kulla makircin kunyata hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta hanyar yunkurin tunbuke shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu daga ofishinsa.

Ya kuma bayyana wani furuci da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi a wani taron kusoshin jam'iyyar APC, a ranar Litinin, na cewar duk masu kudurin satar akwatunan zabe su shirya yin hakan a bakin rayuwarsu, a matsayin daukar mataki da hannu, yana mai cewa kalaman shugaban kasar sun sabawa kyakkyawar demokaradiya ta kasar.

Da ya ke jawabi a wani taron manema labarai a ofishin yakin zaben dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, a Maitama, Abuja, Hon. Dogara ya yi Allah-wadai da zargin da shugaban kasa Buhari da shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole su ka yi na cewar PDP na da masaniyar matakin INEC na dage zabe tun kafin ranar.

KARANTA WANNAN: Jihar Yobe ta yi babban rashi: Mataimakin kakakin majalisar jihar ya rasu

Fadar shugaban kasa da APC na shirin tsige shugaban hukumar INEC -Yakubu Dogara

Fadar shugaban kasa da APC na shirin tsige shugaban hukumar INEC -Yakubu Dogara
Source: Twitter

"Muna sane da cewa suna kokarin yin duk mai yiyuwa na karkatar da hankulan INEC, tare da tunbuke shugaban hukumar da lalata tsare tsaren da hukumar ta yi kawai saboda sun san cewa ba za su iya samun nasara a zaben ba.

"Daga matsayarmu, aika kayayyakin zabe zuwa garuruwan da ba nan ya dace a aika su ba, da gangan ne, soke zirga zirga, da kuma sauran abubuwan da ka kawo tangarda a shirye shiryen hukumar zabe, duk an yi su ne da nufin lalata shirin zaben domin yin magudi.

"Haka zalika muna sane da cewa akwai matsin lambar da INEC ke samu daga manyan jami'an gwamnati da shuwagabannin APC na cewar ta gudanar da zaben duk da cewar ba ta shirya ba. Muna sane da cewa APC na matsin lamba ga shugaban INEC na gudanar da zabe a wasu jahohi da kuma dage zaben a wasu jahohin domin samun banbance banbancen zaben."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel