Dage babban zaben Najeriya laifin Buhari ne - Sanatan Amurka, Chris Smith

Dage babban zaben Najeriya laifin Buhari ne - Sanatan Amurka, Chris Smith

- Chris Smith ya ce dole shugaban kasa Buhari ya dora laifin dage babban zaben kasa a kansa

- Sanatan kasar Amurka ya yi kira na tabbatar da ingantaccen zabe na gaskiya da adalci kamar yadda ta kasance a zaben 2015

- Smith ya ce duk abinda ya faru a Najeriya zai shafi nahiyyar Afirka baki daya kasancewar madubin dubawa

A ranar Asabar ta makon da ya gabata, 16 ga watan Fabrairun 2019, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta dage babban zaben kasa na kujerar shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya zuwa ranar Asabar ta wannan mako.

Mun samu cewa daya daga cikin 'yan majalisar tarayya na kasar Amurka, Chris Smith, ya yi tsokaci tare da bayyana ra'ayin sa dangane da dage babban zaben kasar nan na Najeriya a ranar Asabar, 16, ga watan Fabrairun 2019.

Buhari a fadar shugaban kasar Amurka; Donald Trump

Buhari a fadar shugaban kasar Amurka; Donald Trump
Source: Depositphotos

Chris Smith, dan majalisar tarayya na kasar Amurka ya ce dage babban zaben kasar nan ta Najeriya ba laifin wani bane face na shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da makarraban sa da kuma makusanta.

Mista Smith, ya ce dole ne shugaban kasa Buhari ya dauki nauyi tare da rataya laifin dage babban zaben kasar nan a wuyan sa kasancewar shugaba kuma mai rike da akalar jagoranci na tafiyar da al'amurran kasar sa.

Dan majalisar ya bayyana dalilai da suka kawo cikas gami da koma baya na sanadiyar dage babban zaben da suka hadar da dakatar da Alkalin Alkalai na kasa, Justice Walter Onnoghen, da kuma hare-hare da aka kai kan wasu ofisoshin hukumar INEC a fadin kasar nan.

KARANTA KUMA: 2019: INEC ta musanta rade-radin barazanar rashin tsaro a jihar Adamawa

Bisa ga madogara ta ire-iren wannan dalilai da Ba Amurken ya wassafa, ya ce akwai barazana ta rashin tabbatuwar ingantaccen zabe mai tsarkakken tsarki na gaskiya gami da adalci da ka iya aukuwa yayin babban zabe.

Ya yi kira ga gwamnatin shugaban kasar Amurka Donald Trump da kuma hukumomin tsaro da na leken asiri, da su sanya idanun lura tare da bayar da muhimmancin gaske akan sha'anin Najeriya kasancewar ta madubin dubawa a nahiyyar Afirka.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel