Satar akwatin zabe: PDP ta shiga damuwa a kan kalaman Buhari – Garba Shehu

Satar akwatin zabe: PDP ta shiga damuwa a kan kalaman Buhari – Garba Shehu

A yau, Talata, ne fadar shugaban kasa ta bayyana cewar jam’iyyar adawa ta PDP ta shiga halin damuwa bayan shugaban kasa Muhammdu Buhari ya umarci jami’an tsaro da kar su tausaya wa duk wanda ya yi yunkurin gudu wa da akwatin kuri’u a zabukan da za a gudanar cikin watan Fabarairu da Maris.

Fadar shugaban kasa ta ce kalaman shugaba Buhari gargadi ne ga ‘yan siyasar da su ka mayar da satar akwatun kuri’u ta hanyar amfani da ‘yan daba al’ada a lokutan zabe.

Da ya ke Magana da manema labarai a fadar shugaban kasa, babban mai taimaka wa shugaba Buhari a bangaren yada labarai, Garba Shehu, y aba boyayyen abu ba ne cewar wasu ‘yan siyasa na amfani da ‘yan ta’adda domin su sace akwatin kuri’u sannan su kashe ma su kada kuri’a ko kuma su raunata su.

Ya ce shugaba Buhari ya yi kalamin ne domin tabbatar da cewar ba a cutar da ma su kada kuri’a ba lokacin zabe tare da bayyana cewar ya kamata a jinjina wa Buhari bisa wannan gargadi ga ma su niyyar sace akwatin kuri’u a lokutan zabe.

Satar akwatin zabe: PDP ta shiga damuwa a kan kalaman Buhari – Garba Shehu

Garba Shehu
Source: Facebook

Kazalika, ya nuna rashin jin dadin sa bisa sukar Buhari a kan furucin da ya yi a kan ma su niyyar sace akwati, tare da nuna mamaki a kan dalilin damuwar su da kalaman na shugaban kasa.

A cewar Shehu, “mambobin jam’iyyar adawa, musamman jam’iyyar PDP, ne ke sukar Buhari saboda sun gama shirya yadda za su yi magudin zabe ta hanyar satar akwatin kuri’u.

DUBA WANNAN: Zan kara koma wa wurin da ‘yan Boko Haram su ka kai min hari – Kashim Shettima

Sun fahimci cewar shugaba Buhari ba zai lamunci almundahanar da su ka saba da ita ba wannan karon. Sun nuna abinda su ke niyyar aikata wa,” a cewar sa.

Shehu ya bayyana cewar duk wanda bashi da wata mummunar manufa a kan zabukan da za a gudanar, kalaman Buhari ba za su dame shi ba.

A cewar sa, “kalaman Buhari ba za su tayar da hankalin duk mai son a yi zabe sahihi kuma mai tsafta ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel