Yanzu Yanzu: A China APC ta koyo magudin da za ta yi da na'urar tantance ma su zabe - Atiku

Yanzu Yanzu: A China APC ta koyo magudin da za ta yi da na'urar tantance ma su zabe - Atiku

Dan takarar Shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari dan kama-karya ne.

Atiku ya bayyana hakan ne a wajen taron da jam'iyyar PDP ta gudanar a Abuja ranar Talata.

Sai dai Shugaba Buhari da jam'iyyarsa ta APC ba su ce komai ba kan wannan zargi ba tukuna.

"Na sha fadi cewa idan ana magana a kan mulkin dimokradiyya, Janar Buhari bai yi ammana da shi ba, bai taba yarda da dimokradiyya ba. Mu ne muka fara fafutukar korar soja domin dawo da dimokradiyya. Bai taba shiga fafutikar dawo da dimokradiyya ba.

Yanzu Yanzu: A China APC ta koyo magudin da za ta yi da na'urar tantance ma su zabe - Atiku

Yanzu Yanzu: A China APC ta koyo magudin da za ta yi da na'urar tantance ma su zabe - Atiku
Source: Twitter

"Kuma kamar yadda kuke ganin, ya ari rigar dimokradiyya ya sanya ne kawai domin ya samu mulki ya yi abin da yake yi yanzu; Ya fi kama da dan kama-karya, ba dan dimokradiyya ba," in ji dan takarar shugabancin Najeriyar.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi zargin cewa jam'iyyar APC ta tura wasu mutane kasar China inda suka samu horo kan yadda za su hana na'urar Card Reader "yin sauri" a yankuna da PDP ke da magoya baya da yawa, sannan a sa "na'urar ta yi sauri "a bangarorin da APC ke da magoya baya da yawa.

A cewarsa, "Idan mutum daga yankin kudu maso kudu ko kudu maso gabas ko kuma arewa ta tsakiyar kasar yake, mai yiwuwa ku fuskanci Card Reader maras sauri.

KU KARANTA KUMA: Zan kara koma wa wurin da ‘yan Boko Haram su ka kai min hari – Kashim Shettima

"Amma masu kada kuri'a a yankunan arewa maso yamma da arewa maso gabas da kuma kudu maso yamma, mai yiwuwa Card Reader din su ta yi saurin tantance su. Mun tattara wadanna bayanai mun mika ga kwamitin yakin neman zabe domin su dauki mataki."

Atiku Abubakar ya yi kira ga jami'an tsaron kasar da kada su yi biyayya ga kiran da Shugaba Buhari ya yi cewa duk wanda ya saci akwatin zabe, to a bakin ransa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel