2019: INEC ta musanta rade-radin barazanar rashin tsaro a jihar Adamawa

2019: INEC ta musanta rade-radin barazanar rashin tsaro a jihar Adamawa

- Babbar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, ta musanta rade-radin fuskantar barazana a sanadiyar rashin tsaro cikin jihar Adamawa yayin ake gab da zabe

- Hukumar INEC ta ce ba bu kamshin gaskiya dangane da rade-radin cikas da za ta fuskanta ta fuskar rashin tsaro yayin zaben kasa a jihar Adamawa

- Kwamishinan hukumar INEC reshen jihar Adamawa ya ce ba bu wannan magana domin kuwa ana zaune lafiya da kwanciyar hankali musamman a cikin kwanakin nan.

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC reshen jihar Adamawa, ta yi karin haske dangane da rade-radin barazanar da ta ke fuskanta sakamakon rashin tsaro da ka iya kawo cikas yayin babban zabe.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito cewa, hukumar INEC ta yi musanta rade-radin cewa tana fuskantar barazana ta rashin tsaro da ka iya kawo ma ta cikas yayin babban zaben kasa a jihar Adamawa.

Shugaban hukumar INEC na kasa; Farfesa Yakubu Mahmood

Shugaban hukumar INEC na kasa; Farfesa Yakubu Mahmood
Source: UGC

Kwamishinan hukumar reshen jihar, Kassim Geidam, shine ya yi wannan karin haske a yau Talata, 18 ga watan Fabrairun 2019 cikin birnin Yola. Ya ce za a gudanar da zabe lami lafiya cikin lumana a jihar Adamawa.

Sabanin yadda ake ikirari da yada kanzon Kurege, Gaidam yayin bayyana rashin gaskiyar wannan lamari, ya musanta rade-radin cewa kalubalai na rashin tsaro ka iya kawo cikas wajen gudanar zabe a jihar Adamawa.

KARANTA KUMA: Amurka ta bayyana yadda APC ta yi nasara a zaben 2015

Gaidam wanda ya bayar da shaidar hakan yayin ganawa da manema labarai a birnin Yola, ya ce jihar Adamawa ta ci gaba da kasancewa cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali musamman a kwanakin da muke ciki.

Cikin jawaban sa na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, Gaidam ya kara da cewa, tuni hukumomin tsaro masu ruwa da tsaki suka kwantar da tarzomar da ke yunkurin kunno kai a Arewacin jihar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel