Matsalolin tsaro ba zasu hana gudanar da zaben 2019 ba – Gwamna El-Rufai

Matsalolin tsaro ba zasu hana gudanar da zaben 2019 ba – Gwamna El-Rufai

Gwamnonin jihohin Kaduna, Borno da Adamawa sun tattauna da manema labaru bayan kammala taron majalisar tsaro da suka halarta wanda ya gudana a fadar shugaban kasa tare a shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin jagora.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito zaman ya samu halartar Gwamnan jahar Kano, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, gwamnan jahar Borno, Kashim Shettima, na Adamawa, Jibrilla Bindow, inda El-Rufai ya yi magana da yawun gwamnonin yayin tattaunawa da yan jaridu.

KU KARANTA: Hukumar DSS ta yi amai ta lashe game da gayyatar jami’in INEC daya sabbaba daga zabe

Matsalolin tsaro ba zasu hana gudanar da zaben 2019 ba – Gwamna El-Rufai

Taron majalisar tsaro
Source: Facebook

A jawabinsa, El-Rufai yace gwamnonin sun bayyana halin tsaron da ake ciki a jihohinsu ne ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma sauran shuwagabannin hukumomin tsaro, inda yace gwamna Shettima ne ya bude taro da jawabi.

“Mun fahimci akwai cigaba a halin tsaro a jihohinmu gaba daya, duk da kalubalen da ake samu, kuma wannan ya tattara ne da goyon bayan da gwamnatin tarayya ke bamu na tura jami’an tsaro a duk lokacin da muka bukata, don haka bana ji kalubalen tsaron da muke fuskanta zai hana gudanar da zabe a jihohinmu

“Amma kaga kamar a Borno, akwai kananan hukumomi guda daya zuwa biyu da jama’a zasu yi zabe amma ba a garuruwansu ba, duk wani mai katin zabe zai iya kada kuri’a a karamar hukumarsa ba kamar shekarar 2015 ba da sai dai kowa ya yi zabe a Maiduguri.

“A Adamawa kuwa, baya ga garin Madagali dake kusa da dajin Sambisa, ba’a samu wani babban kalubalen tsaro ba, don haka idan aka tsaurara matakan tsaro za’a iya gudanar da zabe a can din ma. A Kaduna kuma mun nemi a kara mana yawan Sojoji a garuruwan dake fama da yan bindiga.

“Wadannan garuruwan sun hada da Birnin Gwari, Giwa, Chikun da kuma sauran yankunan da suka yi kaurin suna wajen rikicin kabilanci da na addini, tuni muka tsara yadda za muyi wannan aiki da kwamandan rundunar ta 1 na Soja da kwamishinan Yansanda.” Inji shi.

Sauran wadanda suka halarci zaman akwai hadimin Buhari akan harkar tsaro, Babagana Munguno, Ministan tsaro, Mansur Dan Ali, babban hafsan tsaro, Janar Abayomi Olanisakin, sufetan Yansanda Muhamamd Adamu da sauran shuwagabannin hukumomin tsaro.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel