Umarnin Buhari na harbe barayin akwati ya kaucewa tsarin mulki – Dogara

Umarnin Buhari na harbe barayin akwati ya kaucewa tsarin mulki – Dogara

- Shugaban Majalisa Yakubu Dogara ya soki umarnin da Buhari ya bada

- Buhari ya nemi Jami’an tsaro su harbe duk wanda ya taba akwatin zabe

- Kakakin Majalisar Kasar yace dokoki sun yi tanadi na laifuffukan zabe

Umarnin Buhari na harbe barayin akwati ya kaucewa tsarin mulki – Dogara

Dogara yayi tir da umarnin da Buhari ya bada na harbe masu satar akwati
Source: Depositphotos

Mun ji cewa shugaban majalisar wakilai na tarayya a Najeriya, Yakubu Dogara, ya bayyana cewa umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada na harbe duk wanda ya taba akwatin zabe bai dace da dokokin Najeriya ba.

Rt. Hon. Yakubu Dogara yake cewa dokokin Najeriya sun yi duk wani tanadin ukubar da ta dace da wanda aka kama da laifi a lokacin zabe. Buhari dai yana kan bakar cewa jami’an tsaro su kashe wanda aka samu yana satar akwati.

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun kashe Hadimin Gwamnan PDP Ranar Juma'a

Dogara yake cewa kalaman shugaban sun nuna cewa an dawo da mulkin karfa-karfa na soji a Najeriya. Kakakin majalisar yayi Allah-wadai da yadda shugaban kasa na farar hula zai rika irin wadannan kalamai masu mugun hadari.

Kakakin majalisar wakilan ya kuma kara da cewa wannan umarni na shugaban kasa Buhari, ya nuna cewa an ba sojojin Najeriya damar yin ruwa-da-tsaki a cikin harkar zaben Najeriya duk da cewa ba su da wani hurumi a dokar kasa.

Rt. Hon. Dogara yana ganin cewa wannan mataki da Buhari yake nema a dauka a zaben bana, ya sabawa doka da tsarin mulkin kasa domin za a rika kashe jama’a ba tare da sun zubar da jini ba. Tuni dai wasu a APC sun kare shugaban kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel