Hukumar DSS ta yi amai ta lashe game da gayyatar jami’in INEC daya sabbaba daga zabe

Hukumar DSS ta yi amai ta lashe game da gayyatar jami’in INEC daya sabbaba daga zabe

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta janye gayyatar da ta yi ma wani babban jami’in hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, wanda ake zargin sakacinsa ne ya janyo dage zaben 2019, Mista Okechukwu Ibeanu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Mista Ibeanu, shine kwamishinan INEC mai kula da tsare tsare da zirga zirga, sa’annan shine ke wakiltar yankin kudu maso gabashin Najeriya a hukumar, sai dai ana tuhumarsa da sakaci wajen gudanar da aikinsa, wanda hakan yasa dole aka dage zaben 2019.

KU KARANTA: Babban jami’in hukumar INEC da ya yi sanadiyyar zage zabe zai gurfana gaban DSS

Sauran wadanda hukumar ta gayyata da fari sun hada da daraktan kimiyya na INEC, Chidi Nwafor, daraktan saye saye, Ken Ikeagu, daraktan wayar da kawunan masu yin zabe, Osaze Uzzi da kuma mataimakiyar daraktan kimiyya, Bimbo Oladunjoye.

Sai dai ana cikin tsumayin hallarar wadannan manyan jami’an na INEC ofishin DSS dake babban birnin tarayya Abuja da misalin karfe 2:30, sai kwatsam aka samu labarin cewa hukumar ta DSS ta dakatar da gayyatar tasu.

A wani hannun kuma, wata majiya daga hukumar tsaro ta bayyana cewa binciken da DSS taso ta kaddamar bashi da nasaba da batun dage zaben 2019 da hukumar INEC ta yi, sai dai akan wani hira dake yawo, inda aka jiyo wani gwamnan wata jaha dake kudu masu kudancin kasar nan yana ikirarin akwai wasu jami’an INEC dake masa aiki.

Amma a wani yanayi na waiwaye adon tafiya, an bankado wata kasida da Farfesa Ibrahim Jibrin ya rubuta a shekarar 2015 lokacin da aka nada Ibeanu mukamin kwamishinan INEC, inda ya zargeshi da niyyar dabbaka manufofi da muradin kungiyoyin rajin kafa kasar Biyafara a INEC.

A yanzu dai ana nan ana tafka muhawara akan wannan tsohuwar kasida ta Farfesa Ibrahim, inda wasu ke danganta tsaikon da aka samu a zaben 2019 ga burin Ibeanu na tabbatar da manufofin yan Biyafara, wanda hakan har sun fara kiraye kirayen a tsigeshi da taken #INECIbeanuMustGo.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel